1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abu Namu: Matan Najeriya da sana'ar karuwaci a Jamus

Zainab Mohammed Abubakar GAT
January 13, 2020

A titin da ake kira Vulkanstrasse a birnin Duisburg na Jamus, fitaccen wuri ne na dandazon 'yan matan Najeriya da ake fataucinsu zuwa Jamus da sunan aiki da amma ake tilasta wa shiga karuwanci.

https://p.dw.com/p/3W7nZ
Afrika Nigeria Prostitution Flash-Galerie
Hoto: picture-alliance / Ton Koene

A kullum ana samun karuwar matan da ke zuwa Jamus daga Najeriya, akasarinsu wadanda aka yi simogarsu a cewar Barbara Wellner ta Solwodi, wata kungiya da ke taimaka wa 'yan matan da aka shigo da su ta hanyar fatauci da kuma tilasta su karuwanci. 

A cewar Babara dai yawancin wadanda ke da hannu a irin wannan mummunan kasuwancin bil'adama mata ne, a wasu lokuta ma dangin yaran. A matsayin doka a harkar, sukan yi aiki a madadin sauran 'yan Najeriya da ke jan ragamar fataucin a irin kasashen da za a kai yara matan.

Wadannan masu fataucin mutane kan hari irin wadannan yara tun daga yankunansu na asali, sannan a yi karba-karba da su, daga bisani su iso cikin hannun manyan da ake kira "Madams" a Jamus