1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da ziyarar Rice a Britania

March 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bu7C

Kungiyoyi masu kare hakkin jamaa dake adawa da yakin Iraki a Britania,sun bayyana shirinsu na gudanar da bore a yayin ziyarar sakatariyar harkokin waje na Amurka Condoleeza Rice ,cikin wannan makon a kasar.Rice dai zataje Britanian bisa ga gayyata da sakataren harkokin wajen Britania Jack Straw yayi mata.Rahotanni daga London na nuni dacewa Ziyarar da Condoleeza zata kai Blackburn da Liverpool dake yankin arewa maso yammacin Ingila dai,ya harzuka kungiyoyin jamaa.Liverpool dai zai kasance cibiyar aladun gargajiya na turai daga shekarata 2008.Jagoran adawa da yakin Iraki Mark Holt,yace wannan gangamin nasu zai kasance wani babi ne a tarihin wannan yanki nasu.Yace bai kamata Jack Straw da Condoleeza Rice su mayar da kawunansu kamar masu raya aladu ba,bayan kasancewarsu jagoran sanadiyyar asaran rayuka da aladun jamaa a yankin gabas ta tsakiya,musamman Iraki.