1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
April 3, 2020

A wannan makon ma annobar cutar Coronavirus ko COVID-19 da ta addabi duniya, ta sake daukar hankalin jaridun na Jamus a sharhuna da labaran da suka buga kan nahiyarmu ta Afirka.

https://p.dw.com/p/3aOpz
Präsident John Magufuli aus Tansania
Shugaban Tanzaniya John MagufuliHoto: Getty Images/AFP/M. Spatari


A labarin da ta buga mai taken shugaban Tanzaniya da ya yi imani da Allah, jaridar Die Tageszeitung ta ce yayin da a kasashe da dama aka rufe majami’u da masallatai da sauran wuraren ibada saboda hana yaduwar cutar Coronavirus, a Tanzaniya sun kasance a bude bisa umarnin Shugaba John Magufuli, wanda ya shawarci masu ibada da su hallara domin yin addu'o'i tare, yana mai cewa Corona ba za ta iya shiga wurare masu tsarki irin Masallatai da Coci-coci ba.

Cikowa a Masallatai da Majami'u 

Dubun dubatan magoya bayansa ne dai suka halarci Majami'ar Katholika St. Paul da ke babban birnin kasar, inda aka hana su saka wata kariya a fuska ko hannu. A wasu yankuna na kasar ma, Masallatai da Majami'u sun cika da jama'a. Da ma Hukumar Lafiya ta Duniya ta sha sukan matakan gwamnatin Tanzaniya, kuma yanzu ta damu matuka da halin da kasar za ta iya shiga ciki sakamakon take-taken Shugaba Magufuli.


Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung ta leka kasar Senegal tana mai cewa kamar a ko ina a wannan mawuyacin lokaci, a Senegal mayaudara da masu cewa su masana ne da likitocin bogi na damfarar mutane. Jaridar ta ba da misali da wani wai shi Dr. Samba da ya yi wa manyan kamfanoni a Dakar babban birnin kasar tayin yi wa ma'aikatansu gwajin cutar COVID-19. Abin bakin ciki da dama sun fada tarkonsa sun kuma ba shi kudi masu yawa. Sai dubunsa ta cika har ma ya shiga hannun mahukunta. Akwai masu maganin gargajiya da dama da ke ikirarin samun maganin warkar da COVID-19 duk da cewa har yanzu babu riga kafi ko maganin cutar. 

Afrika Senegal Coronavirus Pasteur Institute in Dakar
Duk da kokarin mahukunta, ana samun 'yan damfara a senegalHoto: Getty Images/AFP/Seyllou


A karshe za mu leka birnin Maiduguri na jihar Bornon Najeriya, inda jaridar Frakfurter Allgemeine Zeitung ta labarto yadda jami'ar Maiduguri ke ci gaba da aiki duk da ta'addancin kungiyar Boko Haram. Jaridar ta ce yanzu haka jami'ar na bincike kan musabbabin ta'addancin na Boko Haram. Duk da dan kwarya-kwaryar zaman lafiya a yankin, masanan sun ce dole a yi nazari a kimiyyance na shekarun ta'addancin.

Entrance to Maiduguri University
Hoto: DW

Kin bayar da kai ga 'yan ta'adda

Da ma dai tun a 2011 lokacin da rikicin Boko Haram din ya faro, jami'ar ta yanke shawarar ci gaba da aikinta, domin rufe jami'ar zai zama tamkar mika wuya ne ga ta'asar masu tada kayar bayan. Bisa tallafin masanin kimiyyar wakoki na jami'ar Hildesheim da ke nan Jamus, Nepomuk Riva an yi wani aikin hadin gwiwa da kwararrun masana na Maiduguri, inda suka wallafa wani littafi na wakokin al'ummar yankin na Arewa maso Gabashin Najeriyar. Jami'ar da ta kasance cikin dar-dar na tsawon shekaru saboda rikicin Boko Haram, yanzu ta farfado da aikin hadin gwiwa da takwarorinta na duniya ta kuma karfafa wannan aiki na binciken kimiyya.