1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan jaridun Jamus kan Afirka

Mohammad Nasiru Awal LMJ
June 26, 2020

Dambarwar siyasa a Sudan da bala'in farin dango a yankin gabashin Afirka da kuma annobar coronavirus na cikin batutuwan da suka mamaye sharhunan jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/3eO4v
Abdalla Hamdok
Firaministan gwamnatin hadaka ta Sudan Abdalla HamdokHoto: picture-alliance/AP Photo

Sharhin na wannan makon zai fara ne da jaridar Der Tagesspiegel wadda ta leka kasar Sudan tana mai cewa: Kyakkyawan fata bayan zanga-zangar matasa. Jaridar ta ce kasar Sudan mai yawan al'umma miliyan 40, za ta samu tallafi bayan wani taro ta kafar sadarwa ta Intanet da ya hada kasashen Turai da na yankin Golf da Amirka da kuma kungiyar Tarayyar Afirka domin samun matsayi guda, kan yadda za a tallafa wa kasar da a bara ta kafa gwamnatin rikon karya da ta kunshi fararen hula da sojoji.

Mulkin sojoji da farar hula cikin sauki

Har zuwa watan Afrilun 2019, Sudan na zama wata kasa da duniya ta mayar saniyar ware saboda tsohon shugaban mulkin kama karya Omar al-Bashir da ya shugabanci kasar tsawon shekaru 30, kafin wata zanga-zangar matasa ta yi awon gaba da gwamnatinsa. Da yawa daga cikin masharhanta sun bayyana mamaki yadda gwamnatin hadakar madafun iko tsakanin sojoji da farar hula ke aiki babu wata matsala ta a zo a gani, amma har yanzu fatan da matasa ke da shi na samun ingantuwar rayuwa bai tabbata ba. Saboda haka taron na ranar Alhamis na da matukar muhimmanci ga gwamnatin Firaminista Abdalla Hamdok.
Daga siyasar Sudan sai matsalar farin dango a kasashen gabashin Afirka, inda jaridar Die Zeit ta yi tsokaci tana mai cewa: Tun wasu watanni da suka gabata farin dango suka addabi gonaki a gabashin Afitrka. Ana fargaba a cikin kwanaki masu zuwa za su isa arewacin Afirka, inda za su tabka babban ta'adi. Jaridar ta ce farin da a bara suka afka wa yankin Kahon Afirka, yanzu sun doshi Arewa da yankin Tekun Aden. Hukumar Abinci da aikin gona ta Majalisar Dinkin Duniya na fargabar cewa kamar a bara, a bana ma farin za su iya sake afka wa kasashen Habasha da Somaliya da watakila kasar Kenya. Fata shi ne a samu saukar ruwan sama da yawa a yankin, ta yadda zai rage karfin farin domin a iya yaki da su ta hanyar feshin maganin kashe kwari.

Kenia Heuschreckenplage Symbolbild
Farin dango sun addabi AfiraHoto: picture-alliance/AP Photo/FAO/S. Torfinn

Annobar coronavirus ta shafi yara dalibai

Har yanzu dai annobar Corona na ci gaba da daukar hankalin wasu jaridun na Jamus. A labarin da ta buga mai taken azuzuwan makarantu ta hanyar Internet a Afirka. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce makarantu sun kasance a rufe lokacin coronavirus, amma an koma ba da ilimi ta amfani da fasahar digital.

Liberia leeres Klassenzimmer einer Schule in Monrovia
Coronavirus ta gurgunta karatun yaraHoto: picture-alliance/dpa/A. Jallanzo

Matakin kulle da yawancin gwamnatocin Afirka suka dauka cikin watan Maris don dakile yaduwar coronavirus, ya shafi yara 'yan makaranta kimanin miliyan 300. Ta ce ko da yake yanzu an fara bude wasu makarantun, amma da yawa daga cikin kasashen na Afirka makarantun za su ci gaba da zama a rufe, saboda haka karantarwa ta amfani da Internet ta zama dole. Ko da yake gagarumin ci-gaba ne a fannin ilimin yaran, amma kalilan ne daga cikin al'umma za su ci gajiyarta, domin masu na'urar komfuta da damar samun Internet a Afirka ba su da yawa. Ga kuma matsalar rashin tsayayyen hasken wutar lantarki, baya ga tsadar hanyoyin sadarwa na Internet a nahiyar. Domin ganin an samu yawan wadanda za su amfana da tsarin ilimin ta kafar sadarwa ta Internet, wasu daga cikin gwamnatoci sun shigar da kamfanonin sadarwa cikin harkar domin ganin kwalliya ta mayar da kudin sabulu.