1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus

Mohammad Nasiru AwalAugust 10, 2007

Halin da ake ciki a Darfur ya fi daukar hankalin jaridun na Jamus a wannan mako.

https://p.dw.com/p/BvPA
´Yan gudun hijira a Darfur
´Yan gudun hijira a DarfurHoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

To jama´a barkanku da warhaka. A wannan makon dai taron sasanta marikitan lardin Darfur na kasar Sudan wanda ya gudana a birnin Arusha na kasar Tanzania ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus akan al´amuran nahiyar Afirka. To amma da farko bari mu fara da Saliyo inda a gobe asabar za´a gudanar da zabe na farko tun bayan janyewar sojojin MDD daga kasar. A cikin wani rahoto da ta buga mai taken fargaba game da barkewar sabbin tashe tashen hankula, jaridar General Anzeiger cewa ta yi ana zaman dar-dar gabanin zabukan na shugaban kasa da na ´yan majalisar dokoki. Jaridar ta rawaito mazauna birnin Freetown wadanda suka yi wani maci na neman zaman lafiya suna nuna fargabar dangane da yiwuwar barkewar wani tashin hankali musamman ganin cewa ´yan sanda ka iya bawa jam´iyar SLPP goyon baya yayin da wadanda zasu kaye a zaben ka iya angiza magoya bayan su su ta da tarzoma. Jam´iyun adawa sun kulla kawance don fatattakar jam´iyar SLPP ta shugaba Ahmad Tejan Kabbah wanda ake zargi da cin hanci da rashawa. Tuni dai shugaban jam´iyar APC Ernest Kromah da sauran jam´iyun adawa suka yi barazanar ta da kayar baya idan suka sha kaye a zaben. Ita kuwa a rahoton ta jaridar TAZ cewa ta yi a saboda matsalolin talauci dake ci-gaba da yin tasiri a rayuwar jama´a a Saliyo, sannu a hankali tsofaffin ´yan tawaye na samun karin magoya baya. Jaridar ta ce gabanin zaben a jiya asabar ko-ina ka zagaya a birnin Freetown gungun-gungun ka ke gani na matasa masu zaman kashe wando saboda rashin na yi. Kididdigar MDD ta nunar da cewa kashi 2 cikin 3 na majiya kartfi a kasar ba su da aikin yi. Jaridar ta ce wannan halin ya sa yanzu matasa a kasar ba sa hangen wata kyakkyawar makoma ta rayuwa.

Shin za´a gudanar da zabe a Kodivuwa wato Ivory Coast nan ba da dadewa ba? Taken wani rahoto da jaridar FAZ ta rubuta kenan dangane da jawabin da shugaba Laurent Gbagbo ya yi cewa yana da niyar shirya zaben shugaban kasa a karshen wannan shekara. Shugaba Gbagbo ya nunar da cewa kamata yayi a warware rikicin siyasar kasar ta hanyar gudanar da zabe. Tun a cikin watan oktoban shekarar 2005 aka shirya gudanar da zaben amma aka dage shi. Jaridar ta saka ayar tambaya tana mai cewa ko da yake a cikin makon jiya aka yi bukin sasantawa a birnin Bouake, wanda ya samu halarcin shugaba Gbagbo da FM Guillaume Soro, amma ana iya fuskantar jinkirin gudanar da zaben a wannan shekara kasancewar har yanzu ba´a kammala kwance damarun tsofaffin sojojin ´yan tawaye ba kana kuma hukuma ba zata iya yiwa dukkan jama´ar kasar rajistar zabe ba.

´Yan tawayen Darfur sun amince da bukatu iri daya game da shawarwarin zaman lafiya da gwamnatin Sudan. Wannan dai shi ne taken rahoton jaridar Berliner Zeitung dangane da taron da aka kammala a birnin Arushan kasar Tanzania tsakanin kungiyoyin ´yan tawayen Darfur da gwamnatin birnin Khartoum. Jaridar ta ce wannan matsaya daya da aka samu tsakanin ´yan tawaye ka iya zama mabudin kawo karshen fadan da ake yi a lardin na yammacin Sudan. Ko da yake daya daga cikin jagoran ´yan tawaye Abdelwahid el Nur ya kauracewa taron amma jaridar ta yi fatan cewa mu a wannan karo haka zata cimma ruwa domin an koyi darasi daga kurakuran da aka tabka a tarukan sulhun da suka gudana a baya a birnin Abujar Nijeriya.

Ita kuwa jaridar FR a sharhin da ta rubuta cewa ta yi aski ya kai gaban goshi dangane da shirye shiryen hada kan rundunar hadin guiwa da MDD da kungiyar tarayyar Afirka zasu girke a Darfur. Jaridar ta ce yanzu haka dai kasashe fiye da 13, 8 daga Afirka suka ba da tabbacin ba da karo karon sojoji ga wannan runduna wadda zata kunshi sojoji dubu 26. Ita kuwa jaridar Tagesspiegel cewa ta yi ko da yake akwai haske game da tattauna batun zaman lafiya tsakanin ´yan tawaye da gwamnati a Khartoum amma har yanzu da sauran rina a kaba. Jaridar ta ce samun nasarar wannan taro zai dagora ga wadanda zasu wakilci ´yan tawaye a tattaunawar da zasu yi da gwamnati.