1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu: ANC na shan kaye a zabe

Ahmed SalisuAugust 6, 2016

Babbar jam'iyyar adawa a Afirka ta Kudu wato DA ta samu kan jam'iyyar ANC mai mulki a zabukan kananan hukumomi da aka yi a sassan kasar daban-daban.

https://p.dw.com/p/1JchS
Südafrika Kommunalwahlen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/D. Farrell

Daga cikin wuraren da jam'iyyar ta DA ta samu nasara har da babban birnin kasar Pretoria sai dai ya zuwa yanzu ba a kai ga samun sakamakon zaben a Johannesburg. Masu aiko da rahotannin dai na cewar daga dan abinda aka samu a wasu mazabun da ke Johannesburg wanda shi ne birni mafi girma a kasar, jam'iyyun biyu na yin kankankan. Za dai a samu kamalallen sakamakon zaben ne da misali hudu agogon GMT. Wannan dai shi ne karon farko da jam'iyyar ANC da ke rike da madafun iko ta samu koma baya a zabuka da aka gudanar a kasar tun bayan da aka kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar.