1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu ta dauki mataki kan kamfanin MTN

Gazali Abdou TasawaNovember 2, 2015

Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta Afirka ta Kudu wato JSE ta dauki matakin hana sayar hannayen jarin kamfanin salula na MTN a bisa zargin sayar da hannayen jarin dan kin biyan tara.

https://p.dw.com/p/1GyXS
Mobilfunk Südafrika
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta Afirka ta Kudu wato JSE ta dauki matakin dakatar da izinin sayar da hannayen jarin babban kamfanin salula na kasar ta Afirka ta Kudu na MTN wanda ya ke kamfanin salula mafi girma a nahiyar Afirka.

Hukumar ta JSE ta dauki wannan mataki wanda ya ke na wucan gadi ne a wannan Litinin a bisa zargin kamfanin da sayar da hannayen jarinsa a dai dai lokacin da hukumar kula da kamfanonin salula ta Najeriya ta NCC ke shirin cinsa tarar kudi biliyan biyar da miliyon dari biyu na dalar Amirka a bisa zarginsa da kin mutunta matakin tsinke layikan kira na mutanen da ba su yi rijistar layin nasu ba.

Hukumar JSE ta ce za ta gudanar da bincke domin gano duk wadanda suka rabu da hannayen jarinsu na kamfanin a dai dai lokacin da suka samu labarin ana shirin daukar matakin yin tara ga kamfanin. Tuni dai wannan badakala ta haddasa faduwar darajar hannayen jarin kamfanin na MTN da kashi biyar da digo shida a wannan Litinin.

A watan Agustan da ya gabata ne dai a bisa dalillai na tsaro hukumar kula da kamfanonin sadarwar ta Najeriya ta NCC ta umarci illahirin kamfanonin salula yin rijistan layukan masu aiki da su dama tsinke duk layikan wadanda ba su zo suka yi rijistar ba.