1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Tsakiya: Tallafin horo daga sojin ketare

Mouhamadou Awal Balarabe
May 9, 2017

Bayan shafe shekaru na yakin basasa, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fara samun tallafin horon sojoji daga kasashen waje don tabbatar da doka da oda a cikin kasar. Sai dai ana fuskantar matsalai wajen samar da rundunar.

https://p.dw.com/p/2cgBz
Zentralafrikanische Republik Bangui MINUSCA UN Truppen
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Batun horas da sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya zama tamkar almara a Bangui babban birnin kasar. Ba a san takamaime wadanda za a horas ba tsakanin 'yan tawaye SELEKA da kuma 'yan bindigan sa kai na Anti-Balaka. Dalili dai shi ne rundunar wannan kasa ta tsakiyar nahiyar Afirka bata taba samun sojoji da suka zarta dubu ba duk kuma da fadin da take da shi. Alhali tuni kasashen duniya suka wanke hannunsu daga aikin wanzar da zaman lafiya, tare da dora wannan nauyi kan dakarun na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da za a baiwa horo.

Kungiyar Gamayyar Turai ta rigaya ta bada tallafin da ake bukata wajen horas da sojoji dabarun yaki da tabbatar da tsaro a sassan Afirka ta Tsakiya da ke fama da rikici, shigen tsarin da ta girka a kasashen Mali da Somaliya. Sai dai Tim Glawion na cibiyar GIGA ta Jamus ya ce da kamar wuya haka ta cimma ruwa saboda

"Rundunar sojojin wannan kasa bata taba aiki yadda ya kamata ba a cikin tarihinta, tun ma kafin rikici da aka fuskanta sojojin da ba su fi dubu ba Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke da su. Sannan ma wadannan dakarun sun fi haifar da tsoro a zukatan al'umma saboda kashe-kashen da suke haddasawa."

Sojoji na sintiri a titinan birnin Bangui
Sojoji na sintiri a titinan birnin BanguiHoto: picture-alliance/AA/N. Talel

Tun bayan samun 'yancin kanta a shekarar 1958, galibin shugabannin Jamhuriyar Afirka sun dauki runudunar sojojin kasar tamkar mallakinsu, inda suke nada danginsu da 'yan kabilarsu a manyan mukamai na soji ba tare da samun horo da ya dace ba. Ko da tsohon shugaban kasa Francois Bozize wanda ya kasance hapsan sojojin kasar sai da yayi ta yi gaban kansa a duk lamuran da suka shafi tsaro a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Hakazalika lokacin da kungiyar tawaye ta SELEKA ta kwance mulki a watan Maris na 2013, sojojin kasar ba su yi wani kwazo ba saboda rashin kayan aiki da kuma horo. Akasarin dakarun sun rikide i zuwa sojojin sa kai karkashin kungiyar Anti-Balaka, lamarin ya sa su aikata ta'asa.

Ayar tambaya a nan ita ce wai shin ya dace tsoffin 'yan tawaye da 'yan bindiga su kasance a cikin rundunar sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya? Tuni dai aka riga aka sanya da dama daga cikinsu a kokarin da ake yi na warware musu kaan yaki. Sai dai Evan Cinq-Mars na cibiyar kula da fararen hula a lokacin rikici na ganin cewar bai dace a sanya tsaffin 'yan tawaye cikin sabuwar rundunar kasar ta Afirka ta Tsakiya ba.

Zentralafrikanischen Republik - Flüchtlingslager Benz-Vi
Unguwannin 'yan gudun hijira a BanguiHoto: picture-alliance/dpa/J. Bätz

"Akwai bukatar tabbatar da cewar wadanda suka aikata munanan ayyuka irin su kate hakkin bil Adama ba a dama da su ba ballanta na ma a sanyasu cikin rundunar sojojin."

Sai dai kuma Tim Glawion na cibiyar GIGA ta Jamus ya ce yana da ja a kan wannan batu, inda ya nunar da cewar idan aka fara mayar da wasu tsoffin 'yan tawaye saniyar ware, to lallai ba za a taba nasarar samar da tsayeyyiar runduna a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba, saboda Su dai tsoffin 'yan tawayen ne suka sa sako da lungu na kasar, ma'ana da su ne za a iya cin gari.