1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika ta kudu ta nemi ganawa da Jami'in jakadancin Amirka

Zulaiha Abubakar
January 15, 2018

Kasar Afrika ta kudu ta nemi ganawa da wani kusa a ofishin jakadancin Amirka dake kasar a yau litinin,don wani taron gaggawa akan furucin ‘batancin da shugaban kasar Amirka Donald Trump yayi akan kasashen Afirka .

https://p.dw.com/p/2qref
Südafrika Präsdient  Jacob Zuma
Shugaban Afirka ta kudu Jacob ZumaHoto: Reuters/S. Sibeko

Wannan furuci na Trump ya yi matukar girgiza Kasashe da yawa a fadin duniya musamman ma kasashen Afrika da ya alakanta da kaskanci.

Furucin dai ya janyo Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Tarayyar  Afrika su zargi Trump da rura wutar wariyar launin fata a fakaice duk kuwa da cewar yayi amai ya lashe a cikin wani rubutu da ya kuma yi a shafinsa na Twitter.

Wata sanarwa da ta fito akan taron gaggawar, gwamnatin Afrika ta kudu ta bayyana cewar akwai bukatar dangantaka tsakanin Amirka da Afrika ta kudu ta zamo bisa fahimta da mutunta juna.

A wani ci gaban kuma, ita ma kasar Botswana ta nemi jakadanta dake kasar ta Amirka da ya tambayi Amirka ko kasarsu na cikin kasashen da Trump ya yi wa kudin goro.