1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

March 17, 2006

Halin da ake ciki a Nijeriya na daya daga cikin batutuwan da Jaridun Jamus suka duba

https://p.dw.com/p/BvPz
Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo
Shugaban Nijeriya Olusegun ObasanjoHoto: dpa

Daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan al’amuran Afurka har da halin da ake ciki a Nijeriya dangane da rikice-rikice na siyasa da zama na dardar da ake fama da su a wasu yankunan kasar. Jaridar DIE TAGESZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka inda take cewar:

“A bangaren siyasa dai famar kai ruwa-rana ake yi a game da ta zarcen shugaba Obasanjo, lamarin da daftarin tsarin mulkin Nijeriya bai tanada ba. An kuwa samu mutane da dama da suka rasa rayukansu a zanga-zangar adawa da wannan manufa. Bugu da kari kuma ko da yake akan fuskanci rikici na addini da kan yi sanadiyyar rayukan mutane a kasar ta Nijeriya, shi ma zanen batancin nan da aka buga a kasar Denemark ya sake rura wutar rikicin na addini tare da kisan mutane da dama. A daura da haka an shiga wani sabon yanayi na ta da zaune tsaye a yankin Nijgerdelta, inda aka yi tsawon makonni da dama ana garkuwa da baki ‘yan kasashen ketare. Ita kanta jam’iyyar dake mulki tana fama da sabani sakamakon rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa da kuma binciken wasu gwamnonin da ake tuhumarsu da cin hanci. A sakamakon haka da yawa daga al’umar Nijeriya ke batu a game da wata shekara ta kaddara ta la’akari da zaben kasar da za a gudanar a badi idan Allah Ya kaimu.”

A ranar larabar da ta shige aka gano gawawwakin wasu ‘yan gudun hijira su 18 a gabar tekun tsuburan kanari a kasar Spain, amma a hakika ba wanda ya ba da la’akari da wannan masifar dake ci gaba da wanzuwa a yankin na kasar Spain, inda tun abin da ya kama daga karshen watan fabarairun da ya wuce zuwa yanzu akalla mutane 50 suka halaka, in ji jaridar NEUES DEUTSCHLAND, wadda ta kara da cewar:

“Kasar Spain na shirin yi wa kasar Mauritaniya tayin hadin kai domin ta hana zirga-zirgar kwale-kwale dake dauke da ‘yan gudun hijira daga gabar tekunta. Amma fa halin da ake ciki a nahiyar Afurka yana da sarkakiyar gaske ta yadda ba wani abin da zai iya hana wadannan ‘yan gudun hijira ci gaba da neman tuttudowa zuwa nahiyar Turai. Duka-duka canjin da za a samu shi ne na hanyoyin da ‘yan gudun hijirar ke bi domin shigowa Turai. A shekarar da ta wuce sai da aka bindige wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar a lokacin da suka yi kokarin tsalake shingen da aka shata akan iyaka, sannan su kuma mahukuntan kasar Maroko suka cafke wasu daga cikinsu suka tura su zuwa hamada. Hatta a yankin yammacin Sahara dake karkashin mamayen Moroko akwai daruruwan ‘yan gudu n hijira na kasashen Afurka dake neman kafar tsallakowa zuwa Turai. Wasu daga cikinsu sun fara ratsawa ta Mauritaniya, wadda ke da tazarar kilomita dubu daga gabar tekun tsuburan Kanari na kasar Spain.”

Shirin KTT na tura sojojinta aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Kongo na da nufin zama abin misali dangane da sabuwar rawar da kungiyar ke takawa a siyasar duniya, amma fa a yanzu lamarin na neman daukar wani sabon salo na ba’a kamar yadda jaridar DIE ZEIT ke gani, inda take cewar:

“A sakamakon roko daga MDD kungiyar tarayyar Turai da kuduri niyyar tura sojojinta domin sa ido akan zaben kasar Kongo da za a gudanar nan gaba a wannan shekara. Amma ga alamu murna na neman komawa ciki. Domin kuwa tuni aka lura da matsalolin da kungiyar ke fama da su a kokarinta na hadin kan manufofinta na tsaro, musamman ganin yadda aka sha famar kai ruwa rana akan maganar tura sojojin zuwa kasar Kongo, inda suka kasa fitowa fili, ko dai su amince ko kuma su ki amincewa da rokon daga MDD. Wannan kuwa abin kunya ne ga kungiyar mai fafutukar neman fada a ji a siyasar duniya.”