1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

October 22, 2004

Daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon har da halin da ake ciki a kasar Liberiya, watanni 12 bayan kafa mulkin rikon kwarya karkashin shugaba Bryant

https://p.dw.com/p/BvfI

A wannan makon ma, daidai da makon da ya gabata, jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al’amuran nahiyarmu ta Afurka, kama daga yammaci zuwa gabaci da kuma kudancin nahiyar. Amma da farko zamu duba wani rahoton da jaridar DIE TAGESZEITUNG ta rubuta ne dangane da yadda wasu hafsoshin sojan kasar Kongo da aka kai su kasar Belgium neman horo suka tsere domin zama bakin haure a sassa dabam-dabam na kasar. Jaridar ta ce:

"Murna ta koma ciki a game da wani shirin da aka yi zaton zai zama zakaran gwaji a game da ma’amallar soja tsakanin kasashen Afurka da na Turai da kuma shaidar gudummawar da kasar Belgium ke bayarwa a fafutukar neman zaman lafiyar kasar kongo. Amma ala-tilas aka dakatar da matakin farko da aka gabatar a cikin watan satumban da ya wuce na ba da horo ga hafsoshin sojan kasar kongon saboda hafsoshi 16 daga cikin hafsoshin soja 285 dake neman horon sun tsere suna masu watangaririya a matsayin bakin haure a sassa dabam-dabam na kasar Belgium."

A wani sabon ci gaba kuma, ba zato ba tsammani, a karshen makon da ya gabata aka saki Morgan Tsivangirai, dan hamayyar shugaba Mugabe a kasar Zimbabwe, inda kuma aka kakkabe shi daga laifukan da ake zarginsa da aikatawa. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi sharhi game da haka tana mai cewar:

"Morgan Tsivangirai ya nuna juriya da karfin zuciya a kokarin karya alkadarinsa da shugaba Robert Mugabe yayi, inda aka zarge shi da laifin cin amanar kasa da kuma shirya makarkashiyar kisan shugaban na Zimbabwe. A hakika ba wanda yayi zaton cewar dan hamayyar zai tsira daga wannan kazafin da ake masa, musamman ganin yadda Mugabe ya rika matsin kaimi akan masu shari’ar. Amma fa alkalan dake shari’ar sun yi watsi da karar da aka daukaka, saboda ba ta da wata madogara."

Yau kimanin shekara daya ke nan da aka nada Gyude Bryant domin shugabancin kasar Liberiya, kuma aka shirya gudanar da wani sahihin zabe domin tabbatar da zaman lafiyar kasar, a cikin watan oktoba na shekara ta 2005. Jaridar RHEINISCHER MERKUR tayi bitar halin da Liberiyar ke ciki a yanzun bayan watanni 12 na mulkin rikon kwarya karkashin shugaba Gyude Bryant sai ta ci gaba da cewar:

"A hakika dai babu wata takamaimiyar nasarar da gwamnatin Gyude Braynt zata iya tinkafo da ita a tsakanin watanni 12n da suka wuce. Domin kuwa har yau ana fama da tafiyar hawainiya a kokarin kwance damarar makaman ‘yan sare ka-noke, wadanda da yawa daga cikinsu yara ne matasa. A wasu sassa na kasar kuma ana fama da kungiyoyi na ‘yan ta-kife dake aikata miyagun laifuka. Amma babbar matsalar da ta zama kyar kifi a wuya ita ce ta cin hanci a tsakanin jami’an siyasa da mahukuntan Liberiya."

A taron kolin da suka gudanar a Tripolin Libiya, kasashen Libiya da Masar da Nijeriya da Sudan da kuma Chadi sun yi Allah waddai da barazanar kakaba wa fadar mulki ta Khartoum takunkumi da ake yi. A jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

"Shuagabannin kasashen Libiya da Masar da Nijeriya da Sudan da kuma Chadi sun yi kira ga kasashen yammaci da su taimaka wa Sudan wajen warware rikicinta a maimakon barazanar kakaba mata matakan takunkumi. Kazalika shuagabannin sun yi fatali da shawarar katsalandan soja a Darfur, wanda suka ce wani yunkuri ne na neman yin shisshigi a al’amuran cikin gida na nahiyar Afurka. A bangare guda sun yi kira ga ‘yan tawayen lardin da su yi biyayya ga yarjejeniyar da aka cimma a abujan Nijeriya domin kai taimakon jinkai ga jama’a, sannan ita kuma Sudan a nata bangaren ta ba da shawarar kirkiro wata jihar tarayya mai kwarya-kwaryan ikon cin gashin kanta."