1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ahmadinedjad yayi taron manema labarai

August 29, 2006
https://p.dw.com/p/BulD

Shugaban ƙasar Iran, Mahamud Ahmadinedjad, ya kiri taron manema labarai, inda ya yayi huruci akan al´ammura daban-daban da su ka jiɓanci siyasar dunia.

Shugaban yayi Allah wadai, da rawar da ƙasashen Amurika da Britania ke takawa tun ƙarsehen yaƙin dunia na 2.

Ya ce mafi yawan rigingimmun da ake fuskanta ta fannin yaƙe da yaƙe, da diplomatia sun samo assali, daga shiga sharo ba shanu da Amurika da Britania ke yi, a harakokin cikingida na kasashen dunia.

A dangane da rikicin makaman nuklea,Ahmadinedjad ya jaddada cewar, babu mahalukin da ya issa, ya hanna Iran mallakar husa´a ta zamani, domin samar da makamashin nukleya.

Ya kuma ci gaba da cewa:

Shugaban ƙasar Iran, ya gayyaci Georges Bush na Amurika, zuwa mahaura kai tsaye, ta hanyar talbajan, to amma bada wata wata ba, Amurika ta maida martani ga wannan gayyata.

A ta bakin kakakin gwamnatin Amurika, batun mahaura da Georges Bush,wani sallo ne, na wasa da hankullan jama´a.