1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Suleiman Babayo AS
June 21, 2018

Ahmed Baba ya kasance daya daga cikin manyan malamai na Afirka a karni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari‘a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane.

https://p.dw.com/p/2tSi0
frican Roots Ahmed Baba
Hoto: Comic Republic

Lokacin da Ahmed Baba ya rayu:
An haifi Ahmed Baba a shekarar 1556. Wasu majiyoyi sun ce a Araouane, kimanin kilomita 250 arewa maso yammacin Timbuktu, birnin da ke arewacin Mali. Akwai kuma yiwuwar an haife shi a Timbuktu lokacin birnin na bunkasa a matsayin cibiyar binciken addinin Islama da harkokin kasuwanci na yankin Sahara. Baba ya yi karatu a birnin Timbuktu a wani masallaci da ya yi suna. Bayan ya nuna adawa da mamaye birnin Timbuktu a shekarar 1591 da sarkin Maroko, Ahmed Al-Mansur ya yi, an tasa keyar Baba zuwa Maroko. Lokacin zamansa na shekaru 12, ya ci gaba da harkokin addinin Islama. Ahmed Baba ya koma birnin Timbuktu a shekarar 1608, inda ya rasu a shekarar 1627.

 

Abin da aka san Ahmed Baba da shi:
Lokacin rayuwarsa an san shi da rubuta yarjeniyoyi na shar’ia da ke da dangantaka da addinin Islama ta hanyar rayuwar Musulmai da addininsu. Yau sunan Ahmed Baba na da dangantaka da tunanin lokacin da birnin Timbuktu yake tsakiyar tashe.

 

Mene ne tunanin Ahmed Baba?
Ahmed Baba ya yi kokarin ganin mutanen da suka fito daga kabilu dabam-dabam sun rayu da juna a birnin Timbuktu a lokacin. Yana ganin ilimi zai kawo karshen bambancin kabilanci. 'Yan Maroko da suka kama Baba duk da sun yi masa daurin talala, sun dauke shi a matsayin malami na gani na fada.

 

Ahmed Baba: Shahararren malamin birnin Timbuktu

Cece-kucen da ke kewaye da Ahmed Baba:
Game da batun bauta, Ahmed Baba ya rubuta cewa Musulmai ba za su zama bayi ba ko daga ina suka fito bisa asalin mutum ko launin fata. A lokacin bayi sun kasance rukuni mai muhimmanci na ciniki a birnin Timbuktu. Ya fahimci dokokin addinin Islama a lokacin ta hanyar da ake gani mai cike da gagarumin sauyi, saboda nuna duk masu imani a matsayin suna da matsayi guda a wajen Allah. Amma, Ahmed Baba bai yi tir da cinikin bayi ba, bisa rubutun ya dace a yi cinikin bayi da ba Musulmai ba.

 

Wane abu ne ya janyo ake kaunar Baba har yanzu?
Ahmed Baba ya shahara saboda sanin da yake da shi da kuma basira, ya nuna bajinta kan adawa da mamaya daga Maroko wadanda suka kame garinsa na Timbuktu.

 

Wane abu ne Ahmed Baba ya ce da ake tunawa da shi?
Lokacin da yake zaman hijira a Maroko, Ahmed Baba ya tuna da gida: "O kai ne mai zuwa Gao, ka yi haka ta bin Timbuktu sannan ka fadi suna ga abokaina. Shaida musu gaisuwa daga wanda yake waje, wanda yake ganin kasa da abokai, da 'yan uwa gami da makwabta."

 

Wane abu Ahmed Baba ya bari?
Babbar makarantar koyar da addinin Islama da bincike da ke birnin Timbuktu, tana dauke da rubuce-rubuce kimanin 30,000 kuma na zama daya daga cikin matattara mafi muhimmanci ta Islama da ke kunshe da littattafai da kayayyakin tahirin wadda aka saka sunan Ahmed Baba sannan wani bangare na duniyar Mercury. An dauki Ahmed Baba a matsayin gwarzo a kasar Mali yanzu haka.

 

Wannan bangare ne na shiri na musamman Tushen Afirka "African Roots", shirin hadin gwiwa tsakanin tashar DW da Gidauniyar Gerda Henkel.