1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AI ta zargi yan sandan Najeriya da aiyukan rashin imani

February 5, 2013

A wani rahoton da bai zama abin mamaki ba, kungiyar IA tace rashin imani al'amari ne da ya zama ruwan dare a tsakanin yan sandan Najeriya, musamman a kudancin kasar

https://p.dw.com/p/17YaF
Hoto: Getty Images/AFP

Farin jinin su dai na shirin kan kan kan da kura a tsakiyar cikin dawa. Sun kuma bata ga sarakuna sannan kuma sun ci zarafin talakawan da suke ikirarin karewa a cewar kungiyar Amnesty International mai fafutukar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa da ta fitar da wani rahoto kan yan sanda a cikin tarrayar Najeriya.

Rahoton mai taken ba adalci  har ga mattace dai ya tabo yanda yan sanda suka kai ga hallaka daruruwan yan kasar da basu jiba basu gani ba sannan kuma suka kasa tabbatar da daukar alhakin laifin su. Kungiyar dai ta ambato abun da ta kira babban gibin dake tsakanin yan sandan kasar da kuma aiyyukan ta'asar da ake zargin su da tafka a wurare daban daban na tarrayar Najeriya, ga yansandan da ake yiwa zargi da ruwa da tsaki da kisa da boye suna cikin kasar . Sabon rahoton da yanzu haka ke daukar hankalin alummar tarrayar Nigeria dai  na kuma kara bude ido ga manyan kalubalen dake gaban tarrayar nigeriar kasar dake cikin shekarun tan a 14 bisa turba irin ta demokaradiya amma kuma ke cigaba da fuskantar matsalolin take hakkin alummarta. Barrister Sani Hussani Garun Gabas dai wani lauya ne mai zaman kansa a tarrayar Najeriyar:

Ana dai zargin yan sandan da kisan babban madugun kungiyar Boko Haramun shekaru kusan hudu da suka gabata a wani abun daya kai ga fito na fiton daya hallaka dubban yan kasar sannan kuma ya diga sunanta cikin taswirar kasashen dake takama da ta'addanci a cikinsu. Duk da cewar dai kakakin rundunar yan sandan kasar yaki cewa uffan a bisa sabon  rahoton dai matsayin   kungiyar na zuwa ne dai lokacin da wani fefen bidiyo ke nuna irin lalacewar makarantun horarwar yansandan nigeriar dama tsarin aikin su cikin kasar ta Najeriya da sannu a hankali al'ummarta ke sauya tunanin su daga taken dan sanda abokin kowa. Abun kuma da a cewar Chinedu Nwagu dake zaman babban jami'in kungiyar cleen foundation mai zaman kanta a tarrayar niegriar da kuma ke kokarin tabbatar da kawo sauyi a cikin aikin dansandan ya sanya watsar da yansandan a cikin shara ke zaman babban kuskure ga daukacin kasar ta Nigeria:

DW_Nigeria_Integration2
Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: Katrin Gänsler

Kana bukatar kallon matsalar daga hanyoyi da dama, na farko dai na zaman na halayyar mu ta cewar kana iya yin kisa kasha ba matsala kuma wannan matsala ce tamu gaba daya ba yansanda kadai ba. Akwai kuma matsala ta irin tanadin da yansandan suka samu domin sauke nauyinsu. Wace irin horarwa suka samu ina ga batun kayan aikinsu. Kuma wadanne hanyoyi ke garesu na tabbatar da doka da oda ba tare da amfani da karfi ba:

In zan iya tunawa dai dai yan sandan Nigeria basu da kwararren jami'I na binciken kisa ko daya a cikinsu. In kuma har akwai to shi ko ita sunyi ritaya bara ko kuma zasu yi a cikin bannan nan

DW_Nigeria_Integration-online3
Binciken yan sanda a kan titiHoto: Katrin Gänsler

Abun jira a gani dai na zaman martanin mahukuntan tarrayar Najeriyar da suka dauki alkwarin gyara rundunar yan sandan amma kuma suka karbi jerin rahotnani har hudu  kan gyaran yan sandan a cikin shekaru 14 da suka gabata suka  kuma kulle su cikin teburin sub a tare da aiki kansu ba.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu