1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akalla mutane 3 sun rasu a zanga-zanga a wasu garuruwa na kasar Guinea

February 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuS9
An ci-gaba da gudanar da zanga-zanga a wasu yankuna na kasar Guinea inda aka halaka akalla mutune 3. Mazauna unguwar Bonfi dake Conakry babban birnin kasar sun ce dakarun tsaro sun kashe mutum daya sannan suka jiwa wani rauni lokacin da suka bude wuta akan wasu matasa da suka fara jifa akan wani ayarin motoci da suka yi tsammanin masu rakiyar shugaban kasa ne. Sannan a garin Kankan dake zama matattarar ´yan adawa wani soji ya bude wuta kan masu zanga-zanga inda ya kashe mutum daya sannan shi kuma aka kone shi kurmus. Hakan ta faru ne bayan da shugaba Lansane Conte ya nada wani tsohon na hannun damarsa a matsayin sabon FM, a wani mataki na kawo karshen yajin aikin gama gari da ´yan adawa da kungiyoyin kodago ke yi.Masu adawa da shugaba Conte sun yi zargin cewa sabon FM Eugene Camara, babban jami´i a jam´iyar dake jan ragamar mulki, yana da dangantaka ta kurkusa da masu mulki a kasar saboda haka da wuya a amince da shi.