1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Bashir ya kafa gwamnatin hadin kan kasa

Mahmud Yaya Azare
May 12, 2017

Yayin da ake kokarin samar da sauye-sauyen siyasa da na arziki a Sudan, shugaba Omar Hassan Al-Bashir ya ayyana kafa wata sabuwar gwamnatin hadin kan kasa da ke ci gaba da janyo cece-kuce a kasar.

https://p.dw.com/p/2cs4M
Omar al-Bashir Archivbild 2012
Hoto: picture alliance/abaca

Shugaba Omar Hassan Al-Bashir ya ce wannan sabuwar gwamnatin hadin kan kasar da ya sanar da kafawa, ita ce matashiya ga tabbatar da adalci da zaman lafiya mai dorewar da 'yan kasar suka jima suna fatan gani

"Gamsuwar da muka yi da cewa hadin kan 'yan kasa da zaman lafiya mai dorewa, ba za su samu ba sai da hadin kai da aiki tare tsakanin illahirin jam'iyyun siyasa da bangarori mabanbanta na 'yan kasa, shi ne ya tilasta mana kafa wannan gwamnatin hadin kan kasa, muna fata sauran masu kishin kasa da ke dari dari za su mu tafi tare dasu.”

Sabuwar gwamnatin da ta kunshi Hasbu Muhammad Abdurrahman a matsayin mataimakin shugaban kasa da Bakri Hassan Saleh a kan kujerar Firaiminista da kuma jagororin adawa a matsayin masu bai wa shugaba shawara, a wannan juma'ar ce a ke sa ran za ta yi rantsuwar kama aiki.

Omar al-Bashir in Juba 06.01.2014
Hoto: Reuters

 Shugaban jam'iyya mai mulki a kasar, Ibraheem Mahmud Hamed ya ce, wannan gwamnatin ta ci sunanta ta hadin kan kasa.

"Jam'iyya mai mulki ta saryantar da hakkinta na mamaye madafun iko kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar, a matsayinta na jam'iyyar da ta lashe galibin zabe. Tun daga ministoci da masu ba da shawara da gwamnoni, duk mun saryantar don kishin kasa da neman hadin kai.”

A yayin da galibin 'yan kasar ke maraba da sabuwar hukumar, su kuwa 'yan adawar da suka kauracewa taron kasar da aka karkare bara, cewa suke da ma sun san za a rina. 

"Aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a taron kasa bil hakki, shi ne mafita ga rikicin kasar Sudan, ba sassakewa masu rike da mukamai wuraren zama, in ba haka ba, to ina amfanin taron kasar da aka share shekaru ana yi? idan ba za a aiwatar dashi ba sau da kafa ba.”

Sudanesische Spezial-Polizei erwidert Beschuss von Rebellen
Hoto: picture-alliance /dpa

A kasar ta Sudan da ke da jam'iyyun siyasa da kungiyoyi masu dauke da makamai fiye da 100, masharhanta na ganin zai yi wuya a kafa kowace irin gwamnati ba tare da wasu sun yi korafin ganin an mayar da su saniyar ware ba. Ko da yake, masharhantan sun yi amannar cewa, rage kashe kudi kan sayen makamai da gudanar da ayyukan gwamnati zai iya yin tasiri matuka ga halin kuncin rayuwar da y'an kasar ke fama da shi, fiye da daukin iko tsakanin jagororin mayakan sa kai  da shuwagabannin siyasa.