1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabaab ta sake barazanar kai hari Kenya

Suleiman BabayoApril 3, 2015

Al-Shabaab ta sake barazanar kai hari Kenya yayin da wasu rahotanni ke nuna aka kama mutane biyu daga cikin wdaanda ake zargin sun kai hari kan wata jami'a

https://p.dw.com/p/1F2Wr
Kenia Garissa Universität Anschlag Soldaten Militär
Hoto: Getty Images/AFP/de Souza

Tsagerun kungiyar al-Shabaab na kasar Somaliya masu kaifin kishin addinin Islama sun yi barazanar kai sabbin hare-hare a kasar Kenya, bayan mahukuntan birnin Nairobi sun rufe jami'ar garin Garissa da aka kai wa harin da ya kai ga mutuwar mutane kusan 150.

Kakakin kungiyar Sheikh Ali Mohamud Rage ya fadi haka a wani gidan rediyo mai goyon bayan tsagerun.

Jama'a a garin Garissa na kasar Kenya na ci gaba da neman 'yan uwa da hari kan jami'a ya ritsa da su a birnin da ke yankin arewa maso gabashin kasar. An tabbatar da mutuwar kusan mutane 150, lokacin da maharan na kungiyar al-Shebaab ta kasar Somaliya suka kai harin.

Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce gwamnati tana kara karfafa tsaro domin tunkarar hare-haren 'yan bindiga.

Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya Papa-Roma Francis ya yi tir da farmaki na kasar ta Kenya da ya kai ga mutuwar kusan mutane 150, abin da ya kira da aikin rashin hankali mai muni.