1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alaƙar tashin hankali da siyasa a Najeriya

Usman ShehuJune 24, 2013

Masana sun bayyana cewa 'yan siyasa ne ke haddas, rarrabuwar kawuna ma biya addinai a Tarayyar Najeriya, inda lamarin kan riƙiɗe izuwa mummunan tashin hankali.

https://p.dw.com/p/18vHE
epa03141460 Nigerian youths set up burning barricades and confront the police for their inability to prevent a bomb blast at St.Finbarr's parish church in Jos, Nigeria, 11 March 2012. Reports state at least three people were killed during a suspected suicide car bombing at a Catholic church in the central Nigerian city of Jos. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Wani tashin hankali da ya faru JosHoto: picture-alliance/dpa

Mahalarta wata bita ta yini guda a Jos, sun gano cewa 'yan siyasa a Najeriya kanyi amfani ne addini ne wajen cimma manufofin siyasa, wanda a karshe jama'a ke aukawa cikin tashe-tashen hankula. Wakilin mu Abdullahi Maidawa Kurgwi yace mahalarta a taron bitar, sun kawo shawara kan bukatar fadakar da al'ummar kasa, domin su fahimci salon siyasar zamanin yau.

Mahalarta bitar dai da suka haɗa da kabilu daban-daban, addinai daban-daban, da kuma masu akidu na siyasa da suka saɓawa juna, sun yi mukabalolin game da rikita-rikitar siyasar Najeriya, inda akasari suka lura da irin siyasar zamanin su marigayi Sardauna Sokoto, da kuma irin siyasar zamanin yau. To ko menen maƙasudin shirya taron bitar Hon. Uthman Aliyu, shine shugaban da ya jagoranci kwamitin shirya bitar. "Yana cewar mun kira taron ne domin jan'yo hankulan 'yan Najeriya game da halin da suka sami kansu ciki, inda wasu kan yi anfani da su don cimma burin su, wanda kuma akasarin jama'ar kasa na nuna ƙyama wa shiga zaɓe sakamakon yadda wasu kan nuna son kai a yayin zaɓen"

Christliche Kirche und im Hintergrund Moschee in Abuja, Nigeria. Foto: fotografiert und aus Privatarchiv zur Verfügung gestellt von Katrin Gänsler.
Babbar mujami'ar ƙasa da ke AbujaHoto: Katrin Gänsler

Wani ɗan siyasa daga ƙabilar Igbo Mr. Wilfred Peter Nwayawu, wanda ya halarci taron, yace ya zama dole 'yan siyasar Arewa. su rungumi na kudu, kana na kudanci su ƙaunaci na arewacin Najierya, inko ba haka ba, to zuwa gaba Nijeriya za ta zama 'yar kallo tsakanin kasashen Afirka. "Bai kamata ba muna ware wannan muce shi Bahaushe ne, ko Igbo, ko Bayarbe, domin kuwa irin wannan wariya ta siyasa shi ke jan'yo wa Nijeriya koma baya, don haka idan ba'a ɗauki matakan gyara ba, nan gaba, 'yan Nijeriya ne za su riƙa zuwa neman abinci a kasashe irin su Ghana, maimakon yadda saɓanin hakan a yanzu"

Nigeria Tag der Demokratie (29.05.2013): Nigerias Präsident Goodluck Jonathan und Namadi Sambo, sein Vize-Präsident; Copyright: DW/U. Musa
Jonathan da Sambo a bikin demokraɗiyya najeriyaHoto: DW/U. Musa

To amma masharhanta irin su barrista Solomon Dalong sun koka kan yadda wasu 'yan siyasa kan fake wa da addini don cimma burin su na siyasa. "Akasarin jama'a kan shiga rigar addini ne don neman muƙamai na siyasa, wanda ya zamana wajibi jama'a su gane don gujewa irin waɗan nan mutane"

Kasancewar mata na daga cikin masu shiga mawuyacin hali a rigingimun siyasa da addini, wata fitacciyar 'yar siyasa Hajiya Inna Madina Sani Abubakar, kokawa ta yi game da hali da mata a Nijeriya suka sami kansu cikin wanda ke tilsta su neman mukaman siyasa. "Tace ganin ya zama dole matan ƙasar nan su ƙara tashi tsaye domin kuwa ana barin su baya, ta fannin shugabancin ƙasa, don hatta kashi 35 cikin 100, da ake cewa an ware wa mata, ba su gani ba"

Weithin sichtbar ist die goldene Kuppel der Großen Moschee am 08.11.2008 in der nigerianischen Hauptstadt Abuja. Foto: Wolfgang Kumm dpa +++(c) dpa - Report+++
Babban masallacin ƙasa da ke AbujaHoto: picture-alliance/ dpa

Mahalarta taron dai sun kawo shawarar cewa, kamata ya yi hukumomi a Najeriya su kara wayar da kan jama'a, domin su gane manufofin 'yan siyasar da ke amfani da addini don cimma burin su na siyasa.

Mawallafi: Abdullahi Maidawa Kurgwi

Edita: Usman Shehu Usman