1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamar fito na fito a ƙasar Masar

Usman ShehuAugust 1, 2013

Magoya bayan Mursi sun yi watsi da izinin da gwamnati ta baiwa jami'an tsaro don su tarwatsa sansanin da suka kafa.

https://p.dw.com/p/19I4K
Supporters of deposed Egyptian President Mohamed Mursi take part in a protest at the Rabaa Adawiya square, where they are camping, in Cairo July 27, 2013. At least 70 people died on Saturday after security forces attacked supporters of deposed President Mohamed Mursi in Cairo, Muslim Brotherhood spokesman Gehad El-Haddad said, adding the toll could be much higher. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Dubban magoya bayan Muhammed Mursi dake jerin gwanoHoto: Reuters/Mohamed Abd El Ghany

A ƙasar Masar magoya bayan hamɓararren shugaba Mursi sun ci-gaba da zaman dircen da suke yi a Alƙahira babban birnin ƙasar. Masu goyon bayan Mursin dai sun ci gaba da kasancewa a dandalin da suka taru ne, duk kuwa da izinin da gwamnati ta baiwa 'yan sanda da su kawo ƙarshen gangamin da aka yi. A halin da ake ciki kuwa, yau Alhamis ne ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle zai gana da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya a birnin Alƙahira. A hirarsa da kamfanin dillalcin labaren Jamus na DPA, Westerwelle yace ƙasar Masar babbar ƙawa ce ta fannin tattalin arziki ga Jamus, kuma yace Masar wata mahimmiyar ƙasa ce a yankin Gabas ta Tsakiya bakin ɗaya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu