1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamun kazancewar rikici a mulkin Taraba

March 3, 2014

Gwamnan da ke rikon jihar Taraba ta Najeriya ya ce sai karfi sai ajali kafin ya kyale wasu 'yan fashi na mukami su kwace mulkin da a cewarsa ke hannunsa a yanzu haka.

https://p.dw.com/p/1BIbZ
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Alamun rikici a cikin mulkin jihar ta Taraba dai ya faro ne sakamakon sallamar tsohon sakataren gwamnatin jihar da ake zargi da handume tsabar kudi har Naira miliyan 400 mallakin talakawan da ambaliyar ruwan shekarar bara waccan ta janyo wa asara.

Abun kuma da ya kai ga mataimakin gwamnan dake rikon jihar Alhaji Garba Umar daukar tsumangiyar da ta kai ga fyada irin ta danyar kadanya cikin daukacin majalisar zartarwar da mai gidan nasa kuma gwamna a daka Danbaba Danfulani Suntai.

To sai dai kuma matakin ya kai ga tunzura rikici a cikin jihar inda addini ke neman daukar sawun gaba cikin harkokin jihar inda kuma yanzu haka gwamnatoci biyu ke neman kafa kansu cikin jihar. Abun kuma da a fadar gwamnan dake riko yanzu haka ke barazana ga harkokin mulkin jihar.

“Tun da Maigidana ya dawo daga jinya muka tarar da mutane a ciki da wajen gwamnati da ke kiran kansu "Cabal". Wadannan mutane sun tsaya tsayin daka suna son su kwace gwamnatin su tafi da ita ba tare da sanin Maigidana ba, wanda ni na tsaya na nuna haka ba zai faru ba. Yanzu haka wasu sun bar gwamnatin bana tare da su sannan na wajen ma ba su cika zuwa Taraba ba. In Allah Ya yarda ba mai kwace gwamnatin na, kuma mun nuna mu mutane ne masu rikon amana. In har Maigidana yazo offis ya ce yana son in mayar masa da wannan mulki zan iya mayar masa.”

Gwamnatoci biyu a cikin jiha guda

Kokari na rikon amana ko kuma rikici na kaiwa a cikin baka dai ya zuwa ranar yau jihar ta Taraba dai na da mutane biyu dake ikirarin su ne sakatarorin gwamnatin jihar na halas sannan kuma da manyan hafsoshin da ke tafi da mulki a jihar guda biyu banda kuma wasu jerin kwamishinonin da suka nufi kotu da nufin hana tabbatar da sallamar da gwamnan da ke rikon ya yi da kuma a fadarsu ba ta bisa ka'ida.

To sai dai kuma daga dukkan alamu tuni sabon rikicin ya fara ta da hankulan dattawan jam'iyyar PDP mai mulki a jihar da suka kira yunkurin a matsayin abun da ba za ta sabu ba kuma kokari na cin amanar 'yan Taraba a fadar Isa Tafida Mafindi dan kwamitin koli na jam'iyyar PDP dake wakiltar jihar a yanzu haka.

Yunkurin cin amanar talakawan Taraba

“Mako biyu da suka wuce suka dauki Danbaba suka kaishi Church wai don ya fadi ya warke zai dawo ya ci gaba da mulki, maimakon haka Danbaba ya ce ya raba wa kowa mota da mashin a wannan Church dole aka yanke Speaker aka dawo da shi gida. Mu fa mutuncinmu ake ci, mu da mukatashi da Danbaba mu da muka shugabanci kamfen din tara wa Danbaba kudi a siyasa, mu da Taraba ta sa muke zartarwa na siyasarmu a hedkwatar jam'iyya na kasa. Ina kiran don Allah da Annabi a fuskanci gaskiya a dubi abun da ke faruwa damu a yi abun da kundin tsarin mulki ya ce.”

Gaskiya domin 'yan Taraba ko kuma gwagwarmayar neman ikon mallakin kudin 'yan Taraba dai sabon rikicin dai ya kama hanyar tsaida al'amuran jihar dake dogaro da tarraya wajen kudin shigarta da kuma ke kallon rigingimu iri iri.

To sai dai kuma a cewar Gwamnan dake rikon har yanzu ko a jikinsa game da batun mulkin jihar da a cewarsa ke hannunsa daram dam-dam.

“Gaskiya ina jin ku kuke ganin kamar gwamnati biyu ce in da kun zo Taraba za ku tarar gwamnati daya ce. Su suke zuwa su sameku ku 'yan jaridu su shaida muku gwamnati biyu ce a Taraba amma mu da muke Taraba mun san gwamnati daya ce, ita ce wannan ta Danbaba da nake tafi da harkokinta a yanzu wanda za ta zo karshe a farkon shekara mai zuwa In Sha'Allah.”

Abun jira a gani dai na zaman mafitar rikicin da ke iya kara kazancewa tare da raba kan daukacin talakawan jihar bisa batun addini.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mohammad Nasiru Awal