1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alex Salmond me rajin ganin Scotland ta kafa kasa zai bar kujerarsa

Yusuf BalaSeptember 19, 2014

Bayan da bangaren masu neman ballewa daga Birtaniya a yankin Scotland ya sha kaye jagoran tafiyar ya ce salon siyasar kasar na bukatar sabbin jini.

https://p.dw.com/p/1DFye
Schottland Referendum Alex Salmond 18.09.2014
Hoto: Reuters/Dylan Martinez

Alex Salmond jagoran masu neman ballewa daga Birtaniya daga yankin Scotland ya bayyana cewa zai sauka daga kujerar sa ta shugaban jamiyyar SPN. Wannan yunkuri na shugaban na zuwa ne bayan da yankin na Scotland ya zabi ci gaba da kasancewa karkashin Birtaniya a wata kuri'ar raba gardama da ta kafa tarihi.

Ya fadi a wani taron manema labarai a birnin Edinburgh cewa a wannan sabon salon tafiyar siyasar kasar jam'iyyarsu da 'yan majalisa da ma kasar baki daya za ta so tafiya da sabon jini.

Har ila yau ya bukaci mutanen yankin miliyan daya da dubudari shida da suka zabi ballewa daga kasar ta Birtaniya su matsa lamba wajen ganin mahukuntan sun cika alkawuran da suka dauka wajen ganin yankin na Scotland ya kara samun karfin iko a madadin barin na Birtaniya.