1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ali Bongo ya fara wa'adi na biyu.

September 27, 2016

A kasar Gabon an rantsar da Ali Bongo don fara shugabancin kasar a wa'adi na biyu.

https://p.dw.com/p/2Qe5L
Kenya Gabon - President Ali Bongo bei Pressekonferenz
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Ranzar da shugaban kasar ta Gabon dai ya biyo bayan hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ya yanke,inda ya amince da nasarar Ali Bongo. Wani mazaunin Libreville babban birnin kasar ta Gabon, ya fadawa manema labarai cewa, su kam rayuwarsu ta dame su bawai harkar 'yan siyasa ba. Domin  abin da suke yi walau ta bangaren gwamnati ko 'yan adawa ba komai bane, illah son kansu kawai. "Duk abinda suka yi don kansu ne, mu kuma duk abinda muke yi shi ne, mu jira kura ta lafa a kasar. Muna da iyalai, muna da 'yan uwa, muna da yara, kuma dukansu muna so su je makaranta. A gefe guda su kuma 'yan siyasa ya kamata su fita harkar kasa su yi nasu sha'anin"