1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ali Bongo ya lashe zaben Gabon

Abdul-raheem HassanAugust 31, 2016

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo, zai sake dare mulkin kasar karo na biyu. To sai dai abokin takararsa yayi watsi da sakamakon zaben.

https://p.dw.com/p/1JtHh
Gabun Präsidentenwahl Libreville 27.08.2016 Ali Bongo Ondimba
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Ali Bongo Odinba ya lashe zaben kasar Gabon a hukumance, da tazaran kuri'u kimanin dubu shida ne Ali Bongo mai shekaru 57 ya samu damar darewa kan kujerar shugabancin kasar karo na biyu inda ya samu kashi 49.80 cikin 100 na kuri'un 'yan kasar yayin da abokin takaransa Jean Ping ya samu kashi 48.23 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.

To sai dai tuni Jean Ping ya yi watsi da sakamakon wannan zabe, wanda hakan ya tinzira magoya bayansa suka soma zanga-zangar a ofishin hukumar zaben kasar. A tun shekara ta 2009 ne dai shugaba Ali Bongo Odinba ya dare shugabancin kasar ta Gabon bayan rasuwar mahaifinsa.

To sai dai wakilan kasa da kasa sun ja hankalin jami'an tsaro da su tsaurara matakan tsaro na ganin an takaita tashin tashina donmgudun sake jefa kasar cikin rikicin bayan zabe.