1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alkalan ICC: Gbagbo zai koma gida

Yusuf Bala Nayaya
January 16, 2019

Alkalai a Kotun Hukuntan Manyan Laifuka ICC a wannan rana ta Laraba sun ba da umarni na a saki tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo don ya tafi gida.

https://p.dw.com/p/3BfzA
Niederlande Laurent Gbagbo vor dem Internationalen Straferichtshof in Den Haag
Hoto: Reuters/P. Dejong

Kwana guda bayan da Kotun ICC ta yi watsi da gabatar da karar da aka yi a kan Laurent Gbagbo kan laifukan yaki sakamakon rasa rayukan mutane 3000 da aka yi a kasarsa dalilin barkewar rikici bayan zabe.

Alkalan dai sun wanke tsohon shugaban mai shekaru 73 da haihuwa kan laifukan take hakkin bil Adama da ake zarginsa da su. Magoya bayan Gbagbo dai sun taru a gaban kotun ta ICC a birnin na The Hague inda suka shiga tsallan murna yayin da can mahaifarsa mahukuntan birnin Abidjan ko Shugaba Alassane Ouattara, ya ce dawowar sa kasar ba za ta zama barazana ba ga siyasa. Sai dai ba a kai ga sanin ba ko yaushe ne Gbagbo da na hannun damansa Charles Ble Goude za su bar inda ake tsare da su ba karkashin kotun ta ICC.