1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan gudun hijira sun jefa jama'a cikin yanayin fargaba

Ramatu Garba Baba
March 8, 2019

Dubban 'yan gudun hijirar Sudan da suka nemi mafaka a Nijar, sun nemi gwamnatin kasar da ta gagauta ba su takardar shedar zama don rage radaddin rayuwa, matakin da aka ce na neman tada zaune tsaye ne.

https://p.dw.com/p/3Eh1h
Südsudan Flüchtlinge an der Grenze Uganda-Südsudan
Hoto: Getty Images/AFP/I. Kasamani

Zargin fyade da sace-sace na daga cikin dalilan da suka saka hukumomi kebe 'yan gudun hijirar, amma bayan kwashe lokaci suna rayuwa a sansanin aka soma samun labarin yunkurin tayar da rikici da sunan jan hankulan hukumomin Nijar don basu takardar shedar zaman, amma a cewar Gwamnan na Agadez, Sadou Soloke, da ya ziyarci sansanin, ya ce ba za su amince da duk wani yunkuri na tada zaune tsaye ba, ya kara da cewa, babu wani dalili na matsawa gwamnati kafin ta bayar da takarda, ya shawarci 'yan gudun hijirar da su kwantar da hankulansu har sai an kamalla bincike.