1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Gambiya na zaben 'yan majalisa

Yusuf Bala Nayaya
April 6, 2017

Jam'iyyu tara ne suke fafatawa a zaben 'yan majalisar dokokin Gambiya na wannan rana ta Alhamis ciki kuwa har da jam'iyyar APRC ta Jammeh da jam'iyyar UDP.

https://p.dw.com/p/2amOh
Gambia Wahlen
Hoto: picture alliance/AP Photo/J. Delay

Al'ummar Gambiya na zaben 'yan majalisar dokoki a karon farko tun bayan karshen gwamnatin Shugaba Yahya Jammeh, zaben da ake ganin zai bada dama ga 'yan takarar jam'iyyu su shiga a  dama da su a majalisar, sabanin tsawon shekaru 22 da aka gani kusan jam'iyya guda mai mulki ke kida ta yi awarta a majalisa.

Akwai dai jam'iyyu tara da suke fafatawa da juna a zaben na wannan rana ta Alhamis ciki kuwa har da jam'iyyar APRC ta Jammeh da jam'iyyar UDP. 'Yan Gambiya 880,000 suka cancanci kada kuri'a a zaben da za a fara takwas na safe har i zuwa biyar na yamma. Akwai dai kujeru 53 na 'yan majalisar da jam'iyyu za su nema baya ga biyar da ke zama nadi daga bangaren shugaban kasa.