1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Rasha na zaben 'yan majalisa

September 18, 2016

Wannan zabe dai ana masa kallon zakaran gwajin dafi na makomar jam'iyyar United Russia mai mulki a kasar.

https://p.dw.com/p/1K4Q3
Ukraine Krim Bachtschyssaraj Duma Wahlen Wahllokal Tataren
Zabe 'yan majalisar Rasha a yankin CrimeaHoto: picture-alliance/AP/M. Voronov

Al'ummar kasar Rasha sun fita dan kada kuri'a a zaben 'yan majalisa da ke zama na farko tun bayan da kasar ta Rasha ta mamayi yankin Crimea shekaru biyu da suka gabata.

Kasar ta Rasha dai ta shiga yana yi mara dadi ta fannin tattalin arziki bayan mamayar ta a yankin Crimea, inda kasashen Yamma suka dauki mataki na sanya mata takunkumi. Wannan zabe dai na ranar Lahadi da za a zabi 'yan majalisa 450 na zama gwaji kan irin goyon bayan da jam'iyyar United Russia mai mulki a kasar ke da shi.

Wasu rahotanni dai sun nunar da cewa jam'iyyar ta United Russia farin jininta na raguwa daga kashi 39 cikin dari a watan Agusta inda ya koma kashi 31cikin dari a watan Satimba kamar yadda kididdigar cibiyar Levada mai zaman kanta da ta ji ra'ayoyin jama'a ta nunar.