1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane fiye da 100 sun hallaka sakamakon ambaliyar ruwa

Binta Aliyu Zurmi MNA
July 15, 2019

Mutane fiye da 100 sun hallaka wasu miliyoyi da dama da sun kauracewa gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa a kasashen Indiya da Nepal da kuma Bangladesh.

https://p.dw.com/p/3M7Pv
Indien Überflutungen in Mumbai
Hoto: Reuters/F. Mascarenhas

Alkalumman wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a wasu yankuna na kasashen Indiya da Nepal da kuma Bangladesh sun haura mutum dari. Ko baya ga asarar rayukan da ta haddasa, ambaliyar ta kuma tilastawa miliyoyin mutane barin matsuguninsu.

Yankin Assam da Bihar na Indiya na daga cikin yankunan da wannan ibtila'in ya afkamawa, a cewar wani rahoto da gwamnatin kasar ta fitar sama da kwanaki goma da suka gabata yankin na Assam ke fama da wannan ambaliyar ruwan.