1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa tayi barna mai yawa a Nijar.

September 5, 2014

Wani rahoto da MDD ta fitar kan saukar ruwan sama a Jamhuriyar Nijar, na cewa a kalla mutane da dama ne suka rasu wasu kuma dubunnai suka rasa matsugunnan su.

https://p.dw.com/p/1D7Se
Hochwasser in Sudan
Hoto: EBRAHIM HAMID/AFP/Getty Images

Rahoton kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a kasar Nijar ya ce mutane 28 ne suka rasu, yayin da wasu mutanen dubu 51 suka rasa matsugunnansu sakamakon ruwan sama mai karfi da iska, da rugujewar gidaje da aka fuskanta tun daga watan Yuni da ya gabata a wannan kasa, inda gidaje dubu hudu da 500, tare da Eka 250 na gonaki da garake suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa. Sakamakon farko da gwamnatin Nijar ta fitar ranar 12 ga watan Augusta da ya gabata, ya nunar cewa mutane 12 suka rasu kuma fiye da mutane dubu 27 sun rasa matsugunnansu.

A hannun daya kuma, a daren jiya ne (04.09.2014), kotun tsarin milkin kasar ta Nijar ta tabbatar da halarcin matakin da kwamitin gudanarwa na majalissar dokokin kasar ya dauka dangane da cire rigar kariya ga Shugaban Majalisar dokoki Hama Amadou, da a halin yanzu ya fice daga kasar bisa dalili na ba za a yi masa adalci ba, inda yake gudun hijira a Turai.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Suleiman Babayo