1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da karfin soji kan IS a Yarmuk

Ahmed SalisuApril 9, 2015

Mahukuntan Falasdinu sun ce sun cimma matsaya da takwarorinsu na Siriya don yin amfani da karfin soji da nufin fatattakar 'yan IS daga sansanin 'yan gudun hijirar nan na Yarmouk.

https://p.dw.com/p/1F5Tf
Symbolbild IS Soldaten
Hoto: picture alliance/ZUMA Press/Medyan Dairieh

Ministan kwadagon Falasdinu din Ahmad Majdalani ne ya ambata hakan inda ya ke cewar amfani da karfin soji ne kadai mafita wajen fidda 'yan IS din daga cikin sansanin 'yan gudun hijiarar. Majdalani ya ce dukannin bangarori na kasar ta Falasdinu sun amince da wannan mataki kuma sun ce za su yi aiki tare da nufin cimma wannan nasara da aka sanya a gaba.

Wannan matsaya da aka cimma dai na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar bada agaji ta Red Cross ta bukaci da a dau mataki na gaggawa na ganin an kai ga mazauna sansanin na Yarmouk don bada agaji garesu duba da irin muwaycin halin da suke ciki.