1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da Rediyo wajen yakin neman zabe a Najeriya

Babangida Jibril/ASMarch 17, 2015

Jam'iyyun Njeriya sun dukufa wajen amfani da kafafen watsa labarai musamman gidajen rediyo wajen tallan 'yan takararsu, baya ga kafofin sada zumunta na zamani da suke amfani da su.

https://p.dw.com/p/1EsEX

Yayin da zaben shugaban kasa ke ci gaba da karatowa a Najeriya, jam'iyyu na cigaba da fafutuka wajen nemawa 'yan takararsu kuri'a. Guda daga cikin hanyoyin da suke amfani da su haikan wajen wannan yunkuri ita ce ta gidanjen rediyo duba da yadda 'yan kasar ke sauraron rediyo sosai. Ga misali, jam'iyyar adawa ta APC ko magoya bayanta sun kaddamar da wani gidan radio na sirri wanda don watsa shirye-shiryensa a harshen Hausa.

Girka wannan gida na radiyo dai ya biyo bayan kukan da APC din ta yi na cewar ana dakile kokarinta na yada manufofinta a gidajen rediyo da ke jihohin da ke jam'iyyar PDP ke mulki, to sai dai ita ma PDP din ta ce ba ta samun dama ta tallata manufofita ta gidajen rediyo a jihohin da APC ke rike da su. Shi dai wannan gidan rediyo da APC din ta samar yanzu haka ya na watsa shirye-shiryensa tsakanin karfe bakwai zuwa bakwai da rabi na safe inda a kan sanya wakokin jagoran APC din da sauran mukarraban jam'iyyar.

Afrika Kongo Radio
Rediyo na taka muhimmiyar rawa a rayuwar 'yan Afrika.Hoto: Roberto Schmidt/AFP/Getty Images

Wannan dai ba shi ne karon farko da 'yan adawa ke daukar matakan kafa gidajen rediyo ba, domin a baya kungiyar nan ta NADECO ta kafa wani gidan rediyo da aka yi wa lakabi da Rediyo Kudirat, don haka kafa wannan gidan radiyon za a ce bai zo wa masana tarihin siyasar kasar da mamaki ba kamar yadda wani tsohon dan jarida Abdullahi Abuja ya shaidawa wakilinmu da Minna a jihar Niger Babangida Jibril.

Symbolbild Pressefreiheit in Ruanda - Radio 10 erstes privates Radio in Ruanda
Gidajen rediyo kan shirya muhawarori tsakanin 'yan takara gabannin zabuka a Najeriya.Hoto: Getty Images/AFP/Gianluigi Guercia

Masu bibiyar wannan lamari dai na aza ayar tambaya musamman kan yadda wannan gidan rediyo na APC ya samu lasisin gudanar da harkokinsa. Wannan ne ya sanya DW ta yi kokarin jin ta bakin hukumar NBC da ke kula da kafafen yada labarai a Najeriya don samun karin bayani amma abin ya ci tura, kana ba wani bayani ya zuwa yanzu da aka samu daga gwamnatin tarayyar Najeriya kan wannan batu.