1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da SMS wajen taimakawa masu HIV

July 25, 2014

Kasashen da ke Gabashin Afirka na ci gaba da samun nasara ta hanyar amfani da gajeren sako na SMS wajen taimakawa mutanen da ke dauke da kwayar cutar HIV

https://p.dw.com/p/1Cj36
Aids Medikamente werden in Uganda kostenlos verteilt
Hoto: DW/S. Schlindwein

Ruth Wamboi dai 'yar shekaru 20 ce da haihuwa. Tun a lokacin haihuwarta ta kamu da cutar Hiv. Duk da cewar ba'a san da hakan ba sai da ta yi fama da rashin lafiya mai tsanani lokacin da ta cika shekaru hudu da haihuwa. A asibiti ne aka gano cewar tana dauke da kwayoyin cutar Hiv, wanda tuni ya yi sanadiyyar rayukan Iyayenta da yayarta:

" Na dimauta kwarai da gaske. Na dauka zan mutu. Amma a yanzu ina da fatan cewar zan ci gaba da rayuwa".

A yanzu haka dai Ruth na gudanar da rayuwarta kamar kowa a Kenya, albarkacin Nyumbani, kalmar harshen Swahili da ke nufin gida, wanda suna ne da ke wakiltar wata kungiya da ta shahara wajen kulawa da yara kanan dake dauke da kwayoyin cutar Hiv. Francis Ndegwa shine shugaban cibiyar Kangemi, daya daga cikin unguwar talakawa a birnin Nairobi;

" Ana samun karuwan mace mace, ba wai sanadiyyar Hiv ba, sai dai don wasu matsaloli da ke da nasaba da irin tsananin talauci da mutane ke ciki. A baya kusan kullum yara suna mutuwa. Amma saboda sabbin magunguna da ake dasu, da wuya kaji yaro ya mutu. Hasali ma a kowane wata mura rasa yara biyu ne zuwa uku".

Themenheader AIDS Symbolbild

Kusan yara 500 nedai ake basu kulawa ta musamman a wannan cibiya. Ana basu shawarwari da karfafa musu gwiwa, uwa uba kuma sanin irin magunguna da ya dace su yi amfani dasu, wajen rage radadin kwayoyin cutar ta Hiv. A cewar jagoran shirin Nicolas Makao dai kyauta su ke gudanar da wannan aiki. Sai dai hakan kadai bai wadatar ba;

" Ana shan magungunan ne alokutan da aka kayyade. Muna hulda ne da mutane maras galihu. Muna hulda ne da yara kanana wadanda a wasu lokuta ba zasu iya kulawa da kansu ba, don haka muna dogaro ne da uwayensu, wanda yawancinsu ke gudanar da wasu 'yan kananan ayyuka kamar wanki da sauransu, lokacin da za su dawo gida tunaninsu baya kan batun hadiyar magunguna".

HIV Aids Bekämpfung in Afrika UN Millenniumsziele
Masu fafutukar kare 'yanciHoto: AP

Hakan kuwa ko shakka babu yana da hatsari sosai ga rayuwa, ba wai ga su yaran kadai ba. Har manyan mutane na fuskantar matsaloli wajen shan magungunan rage radadin cutar Hiv akan lokaci. A dangane da hakane kwararru a fannin lafiya suka fitar da wani salo na amfani da gajeren sako ta wayar salula don tunatarwa. Sarah Njoo ita ce ke shugabantar shirin:

" Mutane na amfani da wayoyinsu, layin Airtel yana da araha sosai. Dangane da haka ne muke ganin cewar wannan wani tsari ne da baya bukatar ka kashe kudi mai yawa, musamman idan kwatanta da cewar, sai ka bi mara lafiya har gida don tunatar dashi shan magani".

Wannan tsari dai yana da sauki sosai. Sau daya a mako asibitoci kan aike da gajeren sako ga masu dauke da kwayar cutar, suna tambayar lafiyarsu. Wannan sabon shiri dai yana samun nasara a kasashen yankin gabashin Afrika.

Ana iya sauraron sauti daga kasa

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu