1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da takin gargajiya ga manoma

Wiebke Feuersenger/Salissou BoukariNovember 18, 2015

A shekara ta 2012 sun kaddamar da shiri mai suna ‘Zanj Spice’ na Tanzaniya domin amfanin manoman kayan kamshi da takin gargajiya.

https://p.dw.com/p/1GXYo
Italienische Lebensmittel
Hoto: AP

Bayan ficewar Turawan Portugal, Larabawa daga Oman sun mulki Zanzibar. A lokaci suka fara dashen itatuwa da dama da suka hada da kanunfari a shekarun 1818. Kasar yankin tana da inganci. A karni na 19 icen kanunfari ya samu karbuwa a duniya. Tsibirin Zanzibar tana shiga gaba wajen samarwa. Amma tun bayan faduwar kasuwar, lamura suka sauya. A shekarun 1960 lokacin gurguzu an mayar da tattalin arziki hannun gwamnati. Sai dai lokaci ya wuce da Zanzibar za ta dogara a kan kayan kamshi na abinci, domin kasuwar ta fadi a duniya.

Lokacin da dan kasuwa Michael Haentjes daga Hamburg tare da ma'aikacin kula da raya kasa Friedemann Gille suka ziyarci tsibirin, sun gamsu da yanayin rayuwa. A shekara ta 2012 sun kaddamar da shiri mai suna ‘Zanj Spice’ na Tanzaniya domin amfanin manoman kayan kamshi da takin gargajiya. Kayan kamshin da ake samu sun hada da, kanunfari da citta da barkono da masoro

A Zanzibar ana samun kayan kamshi na abinci kusan kowanne na duniya. Amma lokacin neman wadannan kayan kamshi ya wuce. Patrick Stancilaus Maganga manomi a Zanzibar cewa ya yi. "A baya duk manoma anan sun dogara ne da 'yan yawon bude ido. Idan babu baki babu kasuwa. Domin haka mutane da yawa sun nemi wasu ayyuka."

Tare da wasu manoma 30, Manganga sun kirkiro wata kungiyar gama kai. Tun lokacin manoma ke musayan abubuwa da suka hada da kayan aiki, da abin da kowanne ya sani. Tare sun fadada abin da suke yi, sun fadada abin da suke shukawa matuka, kuma Manganga tare da makwabcinsa Ali Foum sun yi bayanin yadda suka samu nasara. "Mun yanke shawarar amfani da takin gargajiya, wanda ke janyo tashin farashin kayayyakin daga kudin Tanzaniya 15,000 zuwa 20,000."

Karamar kungiyar gama kai da ke garin Stone Town, tana kimtsa kayyakin da aka samu daga takin gargajiya a wannan tsibiri, domin kai wa kasashen Turai. Farooq Mussa ya nuna gamsuwa da hadin kai tsakanin kungiyar da manoma. "Yanzu suna samun kasuwa. Sun san wajen da ake sayar da kayan abincin. A shekarar da ta gabata an samu karuwar abubuwan da aka noma da tsirai kusan 500. Mai yuwuwa nan da shekaru biyu, za su fara noma sabbin tsirrai fiye da 500."

Patrick Manganga ya gina sabon gida da karin kundin da ya samu. Matarsa ta yi farin ciki da haka: "Ina alfahari da shi. Rayuwa na da sauki, iyalai na samun duk abin da suke bukata." Babban dan-sa shi ma dai ya fara dogaro da kai, kuma daga kudin da zai samu nan gaba, Muganga yana son gina masu gida.

Regionalwert AG
Hoto: DW/R. A. Fuchs
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani