1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Jamus za su tsaya kan rikicin Rasha da Ukraine

Muntaqa AhiwaFebruary 10, 2015

Shugabannin Amirka da Jamus sun jaddada sa himma ga kawo karshen rikici a Ukraine

https://p.dw.com/p/1EYsg
Merkel bei Obama 09.02.2015
Hoto: S. Loeb/AFP/K. Lamarque

Shugaban Amirka Barak Obama da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, sun sake jaddata matsayinsu na matsawa kasar Rasha lamba ta fuskar diflomasiyya da ma tattalin arziki don tilastawa Rasha janyewa daga kasar Ukraine. Shugabannin biyu dai sun bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar da suka yi da 'yan jaridu jiya Litinin a fadar White House ta kasar Amirka. Shugaba Obama yayin tattaunawar ya yi reton cewar Amirkar na nazarin ta na taimakawa Ukraine da makaman yaki a karo na farko don kare kanta daga barazanar Rasha.

Sai dai shugabannin biyu, basu sanar da takamaiman dabarun da kasashen yamman za su bi wajen daidaita matsalolin Rasha da Ukraine din ba, musamman ma idan aka gaza cimma daidaito a zaman da ake sa ran yi nan gaba. Angela Merkel ta Jamus da ake ganin ta ke da kyakkyawar dangantaka da shugaba Putin na Rasha dai, ta ce ba ta cire zaton samun nasara a sasantawar diflomasiyyar ba.