Amirka ta dauki mataki kan wasu jami'an Burundi
November 24, 2015Talla
Mutanen da matakin ya shafa sun hada da wasu na kusa da Shugaba Nkurunziza wato Alain-Guillaume Bunyoni, ministan tsaron kasar ta Burundi da kuma Godefroid Bizimana, mataimakin babban daraktan hukumar 'yan sandan kasar da kuma wasu biyu na bangaren adawa da suka hada da Janar Godefroid Niyombare wanda ya jagoranci juyin milkin da bai yi nasara ba, sai kuma Cyrille Ndayirukiye tsohon ministan tsaron kasar.
Wannan mataki na Shugaba Obama ya biyo bayan wani mai kama da irinsa da Kungiyar EU ta dauka a farkon watan Oktoban da ya gabata, kan wasu jami'an kasar ta Burundi.