1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta samu sabon sakataren harkokin waje

December 22, 2012

Shugaban Amirka, Barack Obama ya nada dan majalisar dattawa, John Kerry a matsayin sabon sakataren harkokin wajen kasar.

https://p.dw.com/p/177vH
Hoto: Getty Images

A cikin jawabin da ya yi a birnin Washington, Obama ya ce Kerry ya cancanci rike wannan mukami. Kerry mai shekaru 69 da ke shugabantar komitin harkokin waje a majlisar dattawa zai gaji Hillary Clinton da ke shirin sauka daga wannan mukami da ta ce ba za ta nemi yin wa'adi na biyu ba. Da farko an so ne a ba da wannan mukami ga Susan Rice da ke wakiltar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya. To amma sai 'yan Republikan suka ce su ba za su kada kuri'ar aimicewa da ba ta wannan mukami ba. Shi dai Kerry kwararren masani ne a kan harkokin waje wanda kuma a lokuta da dama ya wakilci Obama a lokutan rikice rikice. 'Yan Republikan suna kuma mutunta shi yadda ya kamata. Kerry shi ne ya tsaya da tutar jam'iyyar Democrat a zaben shugaban kasa a shekarar 2004 , to amma sai ya sha kayi a hannun George W Bush.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal