1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta ta da injunan wasu na’urorinta masu kariya da makamai masu linzami, da shirin ko ta kwana.

June 21, 2006
https://p.dw.com/p/But4

Amirka ta ba da sanarwar ta da injunan wasu na’urorinta na ƙarƙashin kasa, waɗanda ke ɗana rokokin harbo makamamai masu linzamin abokan gaba. Hakan dai ya zo ne bayan damuwar da Washington ke nunawa, game da shirin gwajin makamai masu linzamin nan da ake zaton Korea Ta Arewa za ta yi.

Mahukuntan birnin Pyongyang dai sun ce suna da ’yancin yin wannan gwajin, duk da kiran da kafofin ƙasa da ƙasa ke yi mata na ta dakatad da gwajin. Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Kofi Annan, ya shawarci kasar ta Korea Ta Arewa da ta saurari abin da duniya ke faɗa mata. Amirka kuma ta ce, z ata ɗauki wannan gwajin ne tamkar tsokana. Ana dai zaton cewa, rokan da Korean ke niyyar harbawa, za ta iya lulawa har zuwa tsawon kilomita dubu 6, abin da ke nufin, z ata iya kai jihar Alaska a Amirkan ke nan, idan aka harba ta daga Korean.