1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta ci gaba da taka rawa kan tsaro

February 18, 2017

Mataimakin shugaban Amirka Mike Pence ya tabbatar da goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO karkashin sabuwar gwamnatin Shugaba Donald Trump. Pence ya nunar da haka a gun babban taro kan tsaro a Munich.

https://p.dw.com/p/2XodA
Deutschland Münchner Sicherheitskonferenz 2017
Hoto: Reuters/M. Rehle

Amirka ta tabbatar da shirin ci gaba da taka muhimmiyar rawa bisa tsaro da zaman lafiya karkashin kungiyar tsaron NATO ko OTAN. Mataimakin shugaban kasar Mike Pence ya fadi haka yayin babban taron kasashe duniya kan tsaro da ke gudana a birnin Munich da ke kudancin tarayyar Jamus. Sannan ya nemi Rasha ta mutunta yarjejeniyar shekara ta 2015 da ta kulla da sauran kasashe kan kawo karshen rikicin gabashin Ukraine.

Sannan Pence ya kara jaddada sakon da yake tafe da shi daga Shugaba Donald Trump:

"Shugaban ya bukaci na isar da sakon gaisuwa, kuma a madadin Shugaba Trump ina ba da tabbacin Amirka za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga kungiyar tsaron NATO, babu gudu babu ja-da baya bisa da kawancen tsaron kasashen yankin tekun Atlantika."

Deutschland Münchner Sicherheitskonferenz 2017
Merkel ta tattauna da Mike Pence a gun taron da ke zama karo na 53 a MunichHoto: Reuters/M. Dalder

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tana cikin wadanda suka yi jawabi a zauren taron inda ta nemi aiki tare tsakanin kasashen duniya domin magance matsalolin da ake fuskanta, saboda lamarin ya fi karfin kasa daya ta magance. Akwai shugabannin gwamnatoci daga kasashe daban-daban da ke zauren taron domin duba mafita ga matsalolin cikin kasashen duniya. Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov yana cikin wadanda suka bayyana matsayin kasashensu a zauren taron na birnin Munich.