1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amsoshi: Bayani kan bayyanar Mahadi

Gazali Abdou Tasawa
January 13, 2020

Shirin Amsoshin Takardunku ya ji ta bakin Malaman addinin Islama kan batun bayyanar Mahadin karshen zamani, da dawowar Annabi Isa alaihissalam, da Dujal da kuma Yajuju-Majuju

https://p.dw.com/p/3W7wg
Celle Auftakt Prozess gegen zwei IS-Kämpfer aus Wolfsburg Koran
Hoto: Getty Images/AFP/H. Hollemann

A cikin shirin na wannan mako za ku ji bayani kan wasu muhimman lamurra da addinin Islama ya ambato za su wakana a karshen duniya, da suka hada da bayyanar Mahadin karshen zamani, da dawowar Annabi Isa Alaihissalam da zuwan Dujal da kuma Yajuju-Majuju. Sai dai kasancewa akwai dan sabani tsakanin kan batun zuwan Mahadin tsakanin mabiya tafarkin Sunna da mabiya tafarkin Shi'a, mun ji daga bakin bangarorin biyu. Sai ku saurarin cikakken shirin domin jin karin bayani.