1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bambamcin zaben gwamna a Nijar da Najeriya

Aliyu Abdullahi Imam YB
February 4, 2019

Wai shin mai ya sa kasashe, rainon Faransa irinsu jamhuriyar Nijar ba sa gudanar da zaben gwamnonin jahohi, kamar yadda kasashe rainon kasar Birtaniya suke yi.Ya ma tsarin mulkin nasu yake ne?

https://p.dw.com/p/3Cfwj

Me ya sa kasashe, rainon Faransa irinsu Jamhuriyar Nijar ba sa gudanar da zaben gwamnonin jahohi, kamar yadda kasashe rainon kasar Birtaniya suke yi. To dai mun samu bayanai daga bakin kwararren masani kuma malami a jami'ar Abdou Moumouni da ke Niamey, wato Farfesa Issoufou Yahaya da sakatare na kungiyar masana kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar wanda shi ma malami ne a jami'ar Niamey Dakta Maina Boukar Karte.

A cewar Dr. Karte dai shugaban kasa ke nadi shugaban kasa kuma ke tura wa al'umma. Sai dai kuma a kwai magajin gari wanda shi kuma al'umma ke zabarsa.

Niger Historiker Issoufou Yahaya
Farfesa Issoufou Yahaya Hoto: DW/A. Mahamadou

Shi kuwa Farfesa Yahaya ya ce talaka shi ke da ta cewa game da jin dadin wannan salo na mulki ko akasin haka, kuma wasu na nunar da cewa wannan tsari baya yi masu dadi idan aka kwatanta da takwarorinsu na kasashe da ke magana da harshen Ingilishi.