Amsoshin Takardunku: Ma'anar Maguzanci

Now live
mintuna 06:35
Kalmar Maguzanci na nufin rashin addini, mutanen da basa bautar ubangiji. A kasar Hausawa duk mutanen da basu karbi Musulunci ba ana kiransu da wannan suna a cewar Dr. Tahir Adamu na jami'ar Bayero Kano Najeriya.

Maguzanci na nufin rashin addini, mutanen da ba sa bautar ubangiji. A Makka Annabi S.A.W ya samu mutane Maguzawa kafin su musulunta. A kasar Hausawa duk mutanen da basu karbi Musulunci ba ana kiransu da wannan suna kamar yadda ake gani a wasu sassa na Kano da Jigawa da Katsina a cewar Dr. Tahir Adamu na jami'ar Bayero Kano. Alal misali a Kano wajen Sumaila da Gwarzo, a Tudun Wada a Jigawa a kasar Roni da Katsina a wajen kasar Birci. Duk mutumin da ke zama Bahaushe wanda bai karbi Musuluncin ba akan kira shi da Bamaguje kamar yadda Dr. Tahir Adamu da aka fi sani da Baba Impossible ya yi karin haske.