1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta dora alhakin bacin alamura a Iraki kan Iran,Syria da Alqaeda

October 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bueh

Shugabannin farar hula da na soji na Amurka a Iraqi,sun kira kasashen Iran da Syria da kuma kungiyar AlQaeda a matsayin wadanda suke neman wargaza kasar Iraqi tare da kare Amurka daga tabbatar da kafa demokradiya mai dorewa a kasar.

Cikin kalamai da ake ganin mafiya karfi daga jamian Amurka game da hannun kasashen biyu,jakadan kasar Amurka a Iraqi Zalmay Khalilzad da janar George Casey sun zargi makwabtan Iraqin biyu da laifin goyon bayan zubda jini da akeyi a kasar.

Khalilzad yace wadannan kungiyoyi suna kokarin ganin baa samu nasar a Iraqi ba,saboda a cewarsa suna tsoron ganin kasar taci gaba,inda ya baiyana wasu sabbin matakai da yace Amurkan zata bi don ganin sunyi nasara a Iraqi.