1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta zargi Iran da daurewa yan tawaye gindi a Iraqi

March 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5B

Shugaba Bush na Amurka ya zargi kasar Iran da hannu a cikin hare haren bama bamai da ake kaiwa dakarun sojin kasar dake Iraqi.

Mr Bush ya kara da cewa daurewa yan ta´adda gindi da kasar ta Iran take a hannu daya kuma da kokarin ta na mallakar makamin Aton, abubuwa ne dake kara mayar da kasar saniyar ware a gamayyar kasa da kasa.

Wadannan kalaman dai na shugaba Bush sun zone a yayin jawabin sa na bikin tunawa da Afkawa da Iraqi yaki a matsayin shekaru uku cif.

A lokacin jawabin nasa, shugaban na Amurka ya mayar da hankali ne wajen kafa hujjoji na bukatar kai wannan hari,. A hannu daya kuma da neman goyon bayan Amurkawa.

Kokarin yin hakan dai daga bangaren na Mr Mush, a cewar bayanai yazo ne a yayin da da yawa daga cikin Amurka suka dawo daga rakiyar wannan mataki da kasar ta dauka a kann kasar ta Iraq.