1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ɗage zaɓen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyya

Abdourahamane HassaneJanuary 27, 2016

Nan gaba ne za a bayyana ranar da za a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar wanda tun farko aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi mai zuwa.

https://p.dw.com/p/1Hkv7
Afrika Wahlen in Zentralafrika
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

zaɓen shugaban ƙasar zagaye na biyu wanda za a fafata tsakanin Anicet Georges Dologuele da Faustin Archange Touadera dukkanisu tsofin firaministoci.
Zaɓen wanda aka shirya gudanar a wannan lahadi mai zuwa an ɗageshi har zuwa wani lokacin da za a bayyana a nan gaba saboda dalilan tsare-tsare

A share ɗaya kwamitin tsaro na MDD ya tsawaita takunkumi haramta sayar da makamai ga jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da tsawon shekara guda.