An ba da sakamakon zaben shugaban kasar Mai
August 2, 2013Hukumar ta ce a don haka ya zamo wajibi a gudanar da zaben zagaye na biyu a ranar11 ga wannan wata na Agusta tsakanin shi Keitan da tsohon minisan kudin kasar, Soumaila Cisse da ya yi na biyu. Ga dai yadda Kanal Musa Sinko Koulibali, ministan cikin gidan kasar ta Mali ya ba da sanarwar sakamakon zaben.
Ya ce: "Soumaila Cisse ya samu kuri'u dari shida da dari tara da daya wato kashi 19 da digo 44 daga cikin dari. Ibrahim Boubacar Keita shi kuma ya samu kuri'u miliyan guda da dubu 22 da dari shida da 57 wato kashi 39 da digo 24 daga cikin dari."
Shi dai zaben shugaban kasar ta Mali na zaman wani mataki na maido da kwanciyar hankali da mulkin demokradiya a wannan kasa. Watanni shida ne dai sojojin Faransa suka kwashe suna aiki a kasar domin murkushe 'yan kishin Islama da ke arewacin kasar. Gabanin hakan ne kuma aka hambarar da Shugaba Amadou Toumani Toure.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi