1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bada kyautar Mo Ibrahim ta 2015

March 2, 2015

Shugaban Namibiya mai barin gado Hifikepunye Pohamba ya lashe lambar yabo ta Mo Ibrahim kan shugabanci nagari a kasashen Afirka na wannan shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/1EjvW
Namibia Hifikepunye Lucas Pohamba Staatspräsident
Hifikepunye Lucas PohambaHoto: AFP/Getty Images/J. Watson

Shugaba Hifikepunye Pohamba na kasar ta Namibiya ya kasance na hudu da ya lashe kyautar ta shekara-shekara tun da aka kirkiro a shekara ta 2007 kimanin shekaru takwas da suka gabata, akwai lokutan da babu wanda ya samu nasarar karbar kyautar ta Mo Ibrahim wadda ta kasance kan gaba a kyautukan da ake samu kudi a duniya. Shugaba kwamitin lambar yabon Salim Ahmed Salim da ke zama tsohon Firamnistan Tanzaniya ya tabbatar da zabin da aka yi wa Shugaban ta Namibiya Hifikepunye Pohamba mai barin gado a birnin Nairori na kasar Kenya. Salim Ahmed Salim ya bayyana dalilan da suka bai wa shugaban na Namibiya nasara

Shugabanci na gari na a matsayin matakin samun kyautar.

"Ya yi aiki tukuru wajen inganta demokaradiyya, ya inganta rayuwar mutane. Namibiya karamar kasa ce wadda take da albarkatun kasa, kuma lokacin mulkinsa ya tafiyar da arzikin kasar ta hanyoyin da suka dace. Ya taka rawa wajen tunkarar matsalolin rayuwa kamar yaki da chutar HIV mai karya garkuwar jiki. Namibiya tana cikin kasashen da chutar tafi illa, sannan ya bunkasa ilimi da sauran kyawawan ayyuka wadanda suka zama misali nagari."

Mo Ibrahim
Mo IbrahimHoto: Alex Wong/Getty Images

Shugaban kwamitin ya yaba da irin shugabanci na nagari da Shugaba Pohamba dan shekaru 79 ya nuna a tsawon shekaru 10 na shugabancin kasar ta Namibiya da zai kawo karshensa a cikin wannan wata na Maris. Mutum zai iya lashe wannan kyauta ta Mo Ibrahim ta shekara-shekara idan ya kasance zababben shugaba na Afirka bisa tsarin demokaradiyya, wanda ya nuna shugabanci nagari kuma ya bar ofis cikin shekeru uku da suka gabata, amma babu wanda ya lashe gasar sau hudu a shekara ta 2009, da 2010, da 2012, da kuma 2013. Shugaban na Namibiya mai barin gado Pohamba ya zama wanda ya cancanta sakamakon yadda ya cika sauran ka'idojin. Graham Hopwood babban daraktan cibiyar bincike na harkokin mulki da ke Namibiya, wanda ya nuna gamsuwa da zabin.

Wasu shugabannin Afirka sun lashe kyautar a baya.

Sauran shugabanin da suka lashe wannan kyauta ta Mo Ibrahim sun hada da tsohon Shugaban Mazambik Joaquim Chissano a shekara ta 2007, da Festus Mogae tsohon Shugaban Botswana a shekara ta 2008, da kuma tsohon Shugaban Cape Verde Pedro Pires a shekara ta 2011. Kamar yadda kyautar ta tanada, Shugaba Pohamba mai barin gado na Namibiya zai samu kyautar dala milyan biyar da kuma kudaden da suka kai dala 200,000 duk shekara na fensho kamar yadda aka tsara.

Festus Mogae
Festus MogaeHoto: picture-alliance/ dpa