1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bada sammacin cafke jagororin masu tada zaune tsayen arewacin Mali

February 9, 2013

Wannan sammancin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake batun tattaunawa da wasu daga cikin masu ɗauke da makamai na arewacin ƙasar ta Mali.

https://p.dw.com/p/17bM9
Hoto: AFP/Getty Images

Wata kotu a Bamako babban birnin ƙasar Mali, ta bada sammacin cafke manya manyan ƙusoshin ƙungiyoyi irinsu MNLA masu aware ta abzinawa,da na Mujao da Ansar Dine da ma na Alqa'ida da suka auka wa arewacin ƙasar ta Mali kamun dakarun ƙasa da ƙasa su kore su , inji Daniel Tessogue babban mai gabatar da ƙara na ƙasar ta Mali a cikin wata sanarwar da ya karanta a gidan talabijin na ƙasar a wannan Asabar.
Sanarwar ta ci gaba da cewar ana zargin ƙungiyoyin ne da aukawa ƙasar ta hanyar amfani da makamai tare kuma da kisan gilla a kan dakarun gwamnatin da kuma cin zarafin jama'a haɗe da rushe gine gine mallakar gwamnati.
Daga cikin waɗanda aka bada sammancin su har da Bilal Ag Sherif, magatakardan MNLA da Iyad Agaly jagoran Ansar Dine da Umar Ould Hamda da Sidi Mohamed tare da Sanda Ould Boumama, mambobin Alqa'ida sannan da Cherif Attaher wanda aka fi sani da suna Cherif Ould Tahar na ƙungiyar Mujao.
To sai dai daga cikin waɗanda ake neman ruwa a jallo,har da Algabasse Ag Intala kusa a ƙungiyar Ansar Dine wanda kuma ya canza sheƙa a watan Janairun da ya shuɗe tare da bada hadin kai ga gwamnatin Mali, domin yaƙar abunda ya kira masu fataucin ƙwaya da makamai.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Zainab Mohamed Abubakar