1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bar baya da kura a tsaron arewacin Najeriya

February 5, 2018

Taro na musamman da gwamnatin tarayyar Najeriya gami gwamnonin Arewa maso Gabashin Najeriya suka gudanar ya bankado matsaloli da shiyyar ke fuskanta tare da neman gwamnatin tarayya ta yi musu duba da idon basira.

https://p.dw.com/p/2sAJP
Nigeria Maiduguri Militär Sicherheit Anti Boko Haram 2014
Hoto: picture-alliance/epa

Duk da cewa gwamnatocin Gombe da Yobe sun kauracewa taron wakilai daga sauran gwamnatocin jihohin sun bayyana matsalolin da shiyyar ke fuskanta tare da ba da shawarwari na hanyoyin da za a samu mafita.


Taron wanda ya samu halartar ministan yada labarai da ministan cikin gida da na tsaro da wakilai daga majalisar dokoki ta kasa ya bankado wasu muhimman matsaloli da ake fuskanta a shiyyar da ke neman gwamnatin tarayya ta dauki matakan gaggawa wajen magance su.
A maganar tabbatar da tsaro ministan Mansur Dan Ali ya ce jami'an tsaro sun yi bakin kokarin su: "Lokaci ya wuce da sojanmu zai yada bindiga domin ya tsira da ransa. Yanzu haka dakarunmu da muke alfahari da su sun murkushe Boko Haram kuma a halin yanzu babu wani sashi na Najeriya da ke karkashin ikon su."
 

Symbolbild Soldaten Nigeria
Makudan kudade ne dai Najeriya ke kashewa fannin tsaroHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

To sai dai yanke ta ke shugaban kwamitin kula da tsaro na majalisar dattawan Najeriya Sanata Habu Kiyari wanda dan asalin jihar Borno ne ya musanta wannan ikirari inda ya ce akwai yankin Marte da har yanzu ke karkashin ikon Boko Haram.


Muhammad Bashir Talbari wani da ya halarci taron ya tabbatar da ikirarin sanatan. Sauran matsaloli da aka tattauna a taron sun hada da na makomar 'yan gudun hijira da yadda za a inganta ilimin mata da matsalar shan muggan kwayoyin tsakanin matasa da yadda za a karfafa mata da 'yan kasuwa ta yadda tattalin arzikin kasar zai farfado.


Yayin da wakilan gwamnatin tarayya suka buge da nuna cewa gwamnatin na karfafa matakai na magance wadannan matsaloli tsohon mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai Sanata Ali Ndume ya nuna takaicin karancin kudaden da gwamnatin ke warewa na sake gina shiyyar. Sai dai ministan yada labarai Lai Mohammed ya ce gwamnatin na samar da kudaden ne kwatankwacin samunta.

Nigeria Boko Haram Anschlag in Maiduguri
Harin Boko Haram na ci gaba da lakume rayukan jama'aHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola


Taron wanda aka shirya na tattauanawa tsakanin al'umma da shugabanni bai cimma burin hakan ba don kuwa kalilan daga cikin talakawa da sauran mahalarta ne aka ba su damar yin tambaya ko bada shawara.
Wannan a cewar Muhammad Bashir Talbari ya kashe tagomashin taron. Kusan dai an watse dutse a hannun riga a wannnan taron wanda ke zuwa kwana guda bayan da rundunar Sojojin Najeriya ke wani taron sirri da takwararta ta Jamhuriyar Kamaru domin hada kai don magance matsalar tsaro da ke addabar shiyyar.