1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An biya kudin fansa ko kuma a'a?

October 31, 2013

Bayan sakin Faransawan nan su hudu da aka yi garkuwa da su tun a shekarar 2010 a garin Arlit na arewacin Nijar, ana rade-radin cewa an biya kudin fansa a kansu.

https://p.dw.com/p/1A9oF
Former French hostage Daniel Larribe (2ndR) is welcomed by relatives and French President Francois Hollande (R) on the tarmac upon their arrival at Villacoublay military airport, near Paris, October 30, 2013. Four Frenchmen Pierre Legrand, Daniel Larribe, Thierry Dol and Marc Feret held hostage in the Sahara desert by al Qaeda-linked gunmen for three years left Niger on a French government plane on Wednesday morning. The men, who were kidnapped in 2010 while working for French nuclear group Areva and a subsidiary of construction group Vinci in northern Niger, were freed on Tuesday after secret talks. REUTERS/Jacky Naegelen (FRANCE - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters/Jacky Naegelen

Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta fara labarinta da tambayar shin an biya kudin fansa a kan Faransawan nan hudu da aka yi garkuwa da su a Nijar wadanda aka sako a wannan makon?

"Bayan shekaru fiye da uku ana garkuwa da su, Faransawan su hudu sun koma gida daga Nijar, sai dai jaridar Le Monde ta Faransa ta ce an biya kudin fansa kansu abin da hukumomin kasar suka musanta. Daga samun labarin sakin mutanen ministan tsaron Faransa Le Drian da ministan harkokin waje Laurent Fabius sun tashi nan take zuwa Yamai babban birnin janhuriyar Nijar, inda bayan gajeren jawabi a gaban manema labarai, sun gode wa shugaban Nijar Mouhamadou Issoufou bisa gudunmawar da ya bayar wajen sakin Faransawan. A cikin watan Satumban shekarar 2010 kungiyar Aqmi ta sace mutanen a garin Arlit. Da farko ta nemi a ba ta Euro miliyan 90 kafin ta saki mutanen. Amma a lokacin da ya hau kan karagar mulki shugaban Faransa Francois Hollande ya ce kasarsa ba za ta mika kai ga bukatun 'yan ta'adda ba. Amma jaridar Le Monde ta rawaito cewa bayan tattaunawa ta dogon lokaci, a karshe an biya kudin fansa fiye da Euro miliyan 20."

'Yan tawaye a matakin karshe na yaki

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta leka janhuriyar Demokradiyyar Kongo inda ta labarto cewa kungiyar 'yan tawayen M23 ta bar shelkwatarta ta siyasa a kan iyaka da Yuganda, sai dai ta ce ja da baya ga rago ba tsoro ba ne. Saboda haka gwamnati ta daina murnar cewa ta karya logon 'yan tawayen.

Congolese army soldiers are cheered by residents as they march through Rugare after recapturing it from M23 rebels over the weekend, towards Rumangabo, around 30km (19 miles) from the provincial capital Goma, in eastern Congo Monday, Oct. 28, 2013. The Congolese army, who just one year ago abandoned their posts and fled in the face of an advancing rebel army, succeeded on Monday in taking back a fifth rebel-held town, the city of Rumangabo, in what appears to be a turning point in the conflict. (AP Photo/Joseph Kay)
Hoto: picture alliance/AP Photo

"A ranar Laraba sojojin gwamnati sun kutsa garin Bunagana dake zama mazaunin jagororin kungiyar M23 ciki har da shugabansu Bertrand Bisimwa wanda shaidun ganin ido suka ce ya tsallake iyaka zuwa Yuganda. Wasu rahotanni daga Yugandar cewa suka yi ya tashi ta jirgin saman alikopta zuwa birnin Kampala, dake karbar bakoncin taron neman zaman lafiya tsakanin M23 da gwamnatin Kongo. Katse zaman taron a farkon makon da ya gabata ya sa sojojin gwamnati kaddamar da wani gagarumin farmaki da ya kai ga kwace wani yanki mai girma daga hannun kungiyar M23. Sai dai ba za a iya cewa an ci 'yan tawayen da yaki ba, domin mayakansu ba su tsere zuwa Yuganda ba, sun ja baya ne zuwa kan tsaunuka dake kewayen birnin Bunagana, inda daga nan za su rika kaddamar da yakin sunkuru."

GettyImages 178265177 The head of the UN Stabilization Mission in the Democratic Republic of Congo (MONUSCO) and special envoy of the UN secretary-general, Martin Kobler (R), gives a press conference on August 28, 2013 at the headquarters of the UN peacekeeping mission in Kinshasa. UN attack helicopters joined Congolese government troops in an operation on August 28 against rebels in the east of the Democratic Republic of Congo, the UN peacekeeping force said. The operation against M23 rebels in the hills of Kibati north of the regional capital Goma also involved UN and DR Congo army artillery. AFP PHOTO / JUNIOR D. KANNAH (Photo credit should read JUNIOR D.KANNAH/AFP/Getty Images)
Martin Kobler a taron manema labarai a KongoHoto: Junior D.KannahAFP/Getty Images)

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung tsokaci ta yi a kan halin da ake ciki a gabacin janhuriyar Demokardiyyar ta Kongo inda ta rawaito Majalisar Dinkin Duniya na cewa an kusan karya alkadarin M23 amma 'yan tawayen sun musanta.

Maslaha ta siyasa ce kadai mafita

"Dan diplomasiyar Jamus Martin Kobler wanda tun watanni hudu da suka wuce yake jagorantar tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Kongo ya fada wa Kwamitin Sulhu cewa a fannin soji kam a iya cewa kungiyar 'yan tawayen M23 ta mutu. A makon da ya gabata tattaunawar neman zaman lafiya da ake yi Kampala ta sake gamuwa da cikas, sakamakon takaddamar da ake yi game da bukatar 'yan tawaye na a yi wa shugabanninsu afuwa. Bayan mummunan fadan da aka gwabza tsakanin bangarorin biyu, Mr. Martin ya yi kira da su koma kan teburin shawarwari, domin ta hanyar siyasa ce kadai za a iya warware rikicin na gabacin Kongo."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu