1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude sabon babin zub da jini a Iraqi

January 6, 2014

Ana ci gaba da gwabza fada a kasar Iraqi a garuruwan Falluja da Ramadi a kokarin da sojojin gwamnatin kasar keyi na kwato garuruwan daga hannun 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/1Alqf
Hoto: Getty Images

Tun dai a makon da ya gabata ne aka fara wannan bata kashi tsakanin jami'an tsaro da 'yan tawayen na kungiyar masu kaifin kishin addin dake da alaka da al-Qa'ida, da suka yi amfani da tashin hankalin da ya afku biyo bayan rushe wani sansani na 'yan Sunna masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da jami'an tsaro suka yi a garin Ramadi dake gundumar Anbar. 'Yan tawayen dake gwagwarmaya da makamai dai na karkashin jagorancin kungiyar nan ta Islamic State of Iraq and the Levant (ISIL) dake da alaka da al-Qa'ida wanda kuma suka farma kasar Siriya a kokarin da suke na kifar da gwamnatin Shugaba Bashar Al-assad na Siriyan.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan tawayen na ISIL sun kwace iko da baki dayan garin Falluja dake zaman babban gari a gundumar ta Anbar, yayin da kuma suke rike da wasu sassan Ramadi babban birnin Anbar din, wanda hakan ya sanya aka kori kwamishinan 'yan sandan 'yankin Manjo Janar Hadi Kassar. Kwace iko da garin na Falluja dai ya sanya Firaministan kasar Nuri al-Maliki yin kira ga al'ummar garin da su tashi tsaye domin su kori wadanda ya bayyana da 'yan ta'adda.

'Yan tawayen Iraqi a yayin da suka kwace garin Ramadi
Hoto: Reuters

Yace: "Babu ja da baya har sai mun ga bayan wannan gungun na al-Qa'ida kuma za mu dauki kwakkwaran mataki a kan al'ummar yankin Anbar bisa kasancewar su 'yan al-Qa'ida da suke gudanar da munanan ayyuka".

Rayuka da dama sun salwanta

Kawo yanzu dai kiyasi ya nunar da cewa yakin da ake gwabzawa a gundumar ta Anbar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200 a kwanaki ukun da suka gabata kadai. Dama dai yankunnan Ramadi da Falluja, yankuna ne da masu ta da kayar baya ke da karfi tun bayan shekara ta 2003, yayin da a Falluja ne Amirka ta sha fama da hare-hare a lokacin da ta jibge sojojinta a Iraqin, inda tasha fafatawa da su, wanda kuma aka bayyana da cewa tun bayan yakin Vietnam rabon da ta shiga irin wanna yanayi na yaki.

Sojojin kasar Iraqi a wani wajen duba ababen hawa
Hoto: AP

Yan tawayen dai na kokarin kafa wata kasa dake bin tsarin shari'a a yankunan dake kan iyakar kasashen Siriya da Iraqi. Wani masani kan harkokin kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya Jochen Hippler, ya yi karin haske kan irin karfin da 'yan tawayen na Islamic State of Iraq and the Levents suke da shi a kashen Iraqin da kuma Sirya.

Yace: "Wannan kungiya ta 'yan tawaye na tsakanin kasashen biyu, kuma an basu horo sosai kan harkokin yaki suna da makamai masu yawa ga kwarin gwiwa da kuma hadin kai. A yanzu haka suna da cikakken iko da garin Falluja, suna kuma kara karfinsu a wasu manyan yankunan kasar Siriya da suka hadar da Aleppo da kuma sauran sassa dake gabashin Siriyan".

Shekara ta 2013 ce shekarar zub da jini

Kiyasin Majalisar Dinkin Duniya dai ya nunar da cewa mutane 8,868 ne suka hallaka a Iraqin a shekarar da ta gabata ta 2013, wanda kuma ke nuni da cewa ita ce shekarar da aka fi asarar rayuka a kasar cikin shekaru biyar. Sakataren harkokin waje na Amirka John Kerry ya sanar da cewa Amirka za ta taimakawa sojojin Iraqin a yakin da suke domin fatattakar 'yan ta'addan, sai dai yace Amirkan bata da niyyar sake tura sojojinta zuwa Iraqi. A hannu guda kuma mataimakin babban hafsan Sojin kasar Iran Janar Mohammad Hejazi, ya bayyana cewa Iran din za ta taimakawa Iraqi da kayan aiki da kuma shawarwari.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal